• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lokaci Ya Yi Da Za A Samar Da Sabon Tsarin Mulki – Babban Limamin Coci

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
1 year ago
Mulki

Limamin cocin ‘Anglican Communion’, Reb Henry Ndukuba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wani sabon kundin tsarin mulkin tarayya wanda zai kasance mai amfani da mutane.

 

Ndukuba ya yi wannan kiran ne a wurin bude taron kwamitin cocin Nijeriya da ya gudana a cocin ‘St. Andrew’s Basilica Anglican Church’ a Jihar Inugu.

  • Rahoto Ya Nuna Yadda Noma Ya Samu Koma-baya A Nijeriya
  • Xi Jinping: Inganta Gina Dunkulewar Kabilun Kasar Sin Baki Daya

Limamin cocin a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na cocin, Korede Akintunde ya sanya wa hannu, ya ce kowa ya san cewa Nijeriya na fama da matsaloli da dama, wasu daga cikinsu sun bayyana wanda mabambamtan kungiyoyi suka ankarar, musamman ma na zanga-zangar nuna adawa da rashin shugabanci nagari.

 

LABARAI MASU NASABA

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole

Ya bayyana cewa yayin da majalisar dokokin kasar ta yi aiki mai kyau wajen gyaran kundin tsarin mulkin da aka gada daga sojoji, ya kamata a ce Nijeriya ta samu sabbin dokoki a halin yanzu.

“Wannan sabon kundin tsarin mulki zai yi la’akari da abubuwan da aka riga aka bayyana a tarukan kasa da kuma kiraye-kiraye daban-daban na sake fasalin Nijeriya.

 

Nisantar wannna ya sa har yanzu ba gano bakin zaren matsalolin kasar nan ba,” in ji shi.

 

Limamin cocin ya ci gaba da cewa, makama guda daya tilo da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke bukata ta shimfida shi ne, na tabbatar da mulkin dimokuradiyya da kuma bai wa Nijeriya sabon kundin tsarin mulkin farar hula da ya dace da dimokuradiyya wanda zai magance tushen matsalolin ‘yan kasa.

 

Ya kuma lura da cewa zanga-zangar kyamar rashin shugabanci nagari da aka gudanar duk da rashin jagoranci da manufa ta yi tasiri a wurin gwamnatin tarayya da na jihohi.

“Wannan ya nuna karara cewa jama’a sun gaji da ci gaba da yin alkawurran da gwamnati ta yi na dakile tsadar rayuwa wanda ya haifar da matsananciyar wahala ga magidanta a kasar nan.

“Bugu da kari, kiraye-kirayen da ake yi akai-akai don mahukunta su fahimci halin da ake ciki ko za su sauya salon mulkinsu tare da yin ayyukan da suka makata wajen fitar da al’ummar kasar nan daga kuncin rayuwa.

“Wannan zanga-zangar wani kira ne ga gwamnatoci a dukkan matakai, musamman na tarayya da suka yi kunnen uwar shegu da kukan da jama’a ke yi kan abubuwan da ke ci musu tuwo a karya, domin babu wata gwamnati da za ta iya kafa doka ko hana mutanen da ke fama da yunwa yin zanga-zangar.”

Har ila yau, cocin na Nijeriya ya nuna takaicin yadda wasu masu zanga-zangar suka daga tutocin kasar Rasha a wasu sassan kasar, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, domin ya saba ka’idojin zanga-zangar a Nijeriya, kuma da alama ce ta saba wa tsarin mulki na sauyin gwamnati ba bisa ka’ida ba.

“Mun tabbatar da cewa, wannan hadin gambizar da aka yi ba daidai ba ne, zai iya haifar da rugujewar dimokuradiyyarmu, ya kamata a yi cikakken bincike kan lamarin da magance musabbabin wannan aika-aika da kuma masu ta da zaune tsaye.

“Abin takaici, yana iya yiwuwa akwai alaman tambaya kan wannan lamarin, domin da akwai wata makarkashiya, muna kira da a dauki matakin dakile aukuwar lamarin nan gaba,” in ji shi.

Cocin ta kuma jinjina wa Shugaba Tinubu da ma’aikatan Nijeriya kan rattaba hannu a kan sabon mafi karancin albashi na naira 70,000, inda ta ce wannan abin a yaba ne.

“Duk da haka, muna kira ga gwamnati da ta tsawaita shirinta na biyan ‘yan fansho, wadanda da yawa daga cikinsu na rayuwa ne cikin yunwa, akwai bukatar a sake duba kudaden fansho duk bayan shekaru biyar kamar yadda dokar kasa ta tanada.”

Malamin cocin ya tunatar da masu rike da madafun iko cewa ma’aikatan yau su ne ‘yan fansho na gobe, yayin da ya bukaci majalisar dokokin kasar da tabbatar da biyan kudaden fansho ga wadanda suka cancanta a lokacin da ya kamata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Jonathan
Tambarin Dimokuradiyya

Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole

October 10, 2025
Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya
Tambarin Dimokuradiyya

Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

October 10, 2025
Next Post
Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Al’ummun Duniya Sun Nuna Karin Amincewa Da Kasar Sin

Binciken Ra'ayin Jama'a Na CGTN: Al’ummun Duniya Sun Nuna Karin Amincewa Da Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

October 16, 2025
Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina

Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.