Daga Yusuf Shuaibu,
Me ya jawo hankalinka na neman takarar shuhabacin jam’iyyar APC?
Da farko dai ina gode wa ‘yan Nijeriya na nuna goyon baya a cikin babbar jam’iyyarmu ta APC. Mutane sun dade suna maya mana baya tun a shekarar 2014, kuma yadda abubuwa suke tafiya, jam’iyyar za ta ci gaba da samun goyon baya har gabanin 2023, saboda babu wata jam’iyya da za ta iya karawa da APC tun daga wajen daidaita jinsi da kuma sauran abubuwan da ta aiwatar.
Babban burina ya kasance matasa sun amshi ragamar shugabanci. Akwai wagegen gibi tsakanin dattawa da kuma matasa. A nawa tunanin wannan lokaci ne da ya kamata mu cike gibin. Akwai bukatar mu ja ragamar shugabanci da dora kasar nan a alkiblar da ta dace. Wannan ne ya sa na tsaya takarar shugabancin jam’iyyar APC.
Abin da muka saka a gaba a yanzu haka shi ne, mu amshi ragamar shugabancin jam’iyyar na kasa baki daya. Za mu daidaita abubuwa ta yadda matasa za su fara tsayawa takarar kujerar shugabancin kasa a yanzu. Idan muka samu nasarar daidaita abubuwa a cikin jam’iya, za mu samu damar karfafa wa matasa kwarin gwiwa wajen ci gaban kasar nan.
Ka yi maganar karfafa wa matasa gwiwa ta yadda za su hau kan karagar mulki. To wace hanya wannan burin naka zai iya cika?
Mun fara gudanar da yakin neman zabe tun a watanni ukun da suka gabata. Bayan babban taron farko da muka gabatar na nuna sha’awar tsawa takara, ‘yan Nijeriya wadanda suka yi na’am da cewa wannan lokacin matasa ne sun amince da kudirinmu.
Abubuwan da muke ta kira a kan su tsawan watanni uku shi ne, wannan lokaci ne da matasa za su amshi ragamar shugabanci. Matasa su ne ke da matukar rinjaye a wannan jam’iyyar. Muna da yawan mutane miliyan 41 da suka yi rajista na zama mamba a cikin jam’iyyar APC, bisa wannan al’kaluma, akwai matasa sama da miliyan 30.
Dun daga zaben shugabannin kananan hukumomi na jam’iyyar da kuma mataki na jiha ya nuna cewa, matasa sun bayar da gagarumar gudummuwa. Wannan ne ya ba mu kwarin gwiwa tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar a mataki na taratyya kuma za mu sami nasara.
Ina mai tabbacin cewa za mu sami nasarar lashe wannan takara, saboda matasa su ne mafi rinjaye a cikin jam’iyyar. Bisa irin yakin neman zabe da muke gudanarwa a kasa, ina tabbatar da cewa ko a yau aka gudanar da wannan zabe, to mu ne zamu samu nasara.
Mutane suna yawan magana a kan mayan mutane da suke da kudi. Su waye wadannan mutane? A ko da yaushe wadannan mutane su ma suna bukatar samun mutane duk da suna da kudaden da za su rarraba a kan tituna. Mutane ne wadanda suke kokarin ganin hakarsu ta cimma ruwa. Wadannan manyan ba sa ba mu tsoro saboda abin da muka sani shi ne, wannan lokaci ne da za mu amsa ragamar shugabanci. Ana maganar sauya alkibla ba wai manyan mutane masu kudi ba.
Idan aka duba abubuwan da suke faruwa a cikin shekaru biyu zuwa uku, za a ga cewa wannan lokaci ne da za a bai wa matasa dama. Ba wai maganar kudi ba ne. akwai wasu mutane da suke da kudin, amma ba su iya gudanar da harkokin siyasa ba yadda ya dace. Siyasa ta dogara ne da yadda aka gudanar da ita domin samun kyakkyawan sakamako. Na san abin da zan yi har in samu nasarar lashe zabe. Na taba rike shugaban matasa a karamar hukumata, ida daga cikin mamba a bangaren matasa na CPC, na kasance daya daga cikin kungiyar yakin neman zaben Marigayi Sam Nda-Isaiah da kuma kungiyar yakin neman zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015 da 2019. Na san yadda abubuwa suke tafiya. Shugaban kasa ya fitar da kudi ne kafin aka zabe shi? Ko kadan magana ce ta akida, wannan magana ce ta haduwar ra’ayoyin ‘yan Nijeriya wadanda suka yi kokarin kawo shi kan karagar mulki ta hanyar zabensa, kuma ni ma ta wannan hanya ce zan lashe zabe. Ba na tsoron wani da ke neman wannan kujera saboda kowa yana neman mutane ne. Kowa yana da manufofinsa da zai tallafa wa mutane da zai iya janyo ra’ayin har su yarda da bukatarsa.
Ka yi maganar kana cikin tawagar yakin neman zaben mamallakin Kamfanin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah wanda shi jigo ne a cikin jam’iyyar APC. Kan cewa shi ya yi imani da babbar dabara. Ta yaya za ka iya cika manufar mai gidanka, Nda-Isaiah wajen kawo ci gaba a jam’iyyar wanda shi ya taba futowa takarar shugaban kasa a APC?
Dole a cikin siyasa ya kasance kana da uban-gida. Marigayi Sam Nda-Isaiah yana daga cikin uban-gidana a cikin harkokin siyasa. Duk lokacin da na tuna da shi, babbar dabara nake tunawa da shi. Ba a bukatar yin yakin neman zabe wajen daukar fusta. Marigayi Sam Nda-Isaiah ya koya mana yadda za mu gudanar da yakin neman zabe. Idan mutun yana neman takara, to dole ya kasance ya san abin da zai fada wa mutane kuma har su zabe shi. Wannan dalilin ya sa na fito takarar neman shugabancin jam’iyyar APC kamar yadda kowa ya sani a kan hakan.
Na kasance ina da ajandoji guda hudu wadanda suka hada da gagarimin kawo sauyi a cikin jam’iyyar. Dole ne mu sauya akalar jam’iyyar ta yadda za su iya bayyana wa ‘yan Nijeriya cewa wannan jam’iyya ce da za ta kai su tudun muntsira. Haka kuma ya kasance jam’iyyar ita ce kololuwar jam’iyya a cikin siyasar Nijeriya. Dole mu girmama manufofin jam’iyyar. Ita dai jam’iyya ta kasance a samu nadin kai ta yadda kowa zai girmama dokokinta. Ta hakan ne jam’iyya za ta kasance mafi kololuwa. Ya kuma kasance ana bin ka’idojin dimokuradiyyar cikin jam’iyya. Muna bukatar gina babbar tsarin dimokuradiyyar cikin jam’iyya ta yadda duk wanda ya shiga jam’iyyar da masu tsawa takara za su martaba ta. Haka kuma dole za a tabbatar an bi tsarin kudin mulkin jam’iyya. Akwai kuma inganta tsarin jam’iyyar. Idan muka samu nasarar darewa kan shugabancin jam’iyyar, za mu kawo tsarin da duk wanda ya yi aiki tukuru a wannan jam’iyyar, to za a saka masa daidai da aikinsa. A halin yanzu dai, APC yi alkawarin cewa duk wanda ya yi wa jam’iyyar hidima, to shi ma za a saka masa daidai da aikinsa.
Akwai rahonnin da ke cewa jam’iyyar APC ta rabu gida-gida. Kana tunanin wannan ba zai shafi jam’iyyar ba?
Na fada maka cewa ina da tabbacin lashe wannan zabe duba da irin mutanen da suka tsaya takarar neman shugabancin jam’iyyar. Sun dade a cikin jam’iyyar. Wa kake tunanin zai iya bar wa wani? Amma idan aka kale ne a matsayina na matashi mai jini a jiki za a ga cewa zan iya jan ragamar jam’iyyar. Ina tunanin dukkaninsu za su amince wa Mohammed a matsayin wanda zai jagoranci jam’iyyar, ya kamata su kasance masu bayar da shawarwari da kuma ruwa da tsaki a wannan lamari. Na tuntube su lokacin da muka gudanar da taron. Na bayyana musu cewa ina da muradin shugabancin jam’iyyar kuma ina neman goyan bayansu. Na tabbata idan suka ga uwar bari za su yi hakan.
Kana takarar shugabancin jam’iyyar APC da take fama da rikice-rikice. APC ta dade tana fama da rikicin shugabanci wanda ta kai har Shugaban kasa Buhari ya fito a gidan talabijin yana gargadin ‘ya’yan jam’iyyar a kan su hada kai, idan ba haka ba kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta samu nasarar lashe zaben 2023. Me za ka ce game da wannan lamari?
Ina son mutane su sani cewa babu jam’iyyar da ba ta fama da rikicin cikin gida. Ba abin mamaki ba ne idan mai girma shugaban kasa ya yi wannan gargadi, saboda shugaban kasa ba wai ya kasance dan jam’iyya ba ne kadai shi shugaban jam’iyyar ne. Yana kokarin ya tayar da mu daga dogon barcin da muke yi wajen yin abubuwan da suka dace a cikin jam’iyyar ganin yadda wasu lamura ke faru a cikin jam’iyyar. Dole ne ya fadakar da ‘ya’yansa wajen gabin sun gudanar da abubuwan da ya dace su yi.
A halin yanzu, dukkan ‘ya’yan jam’iyyar sun tashi daga dogon barcinsu. Kwamitin riko na jam’iyyar sun gudanar da abin da ya dace na shirya babban taron jam’iyya a ranar 26 ga watan Fabarairun 2022, sannan sun fara gyara abubuwa ta yadda za a tabbatar da abubuwa sun tafi kan tsari. Wannan haka yake faruwa a cikin harkokin siyasa, saboda dole ne a samu bambancin ra’ayi. Dole ne a sha wahala wajen hada ra’ayoyi a wuri daya. Don haka ina tunanin jam’iyyar ta dawo daga cikin hayyacinta. Za mu gudanar da babban taron jam’iyyar bayan nan kuma mu fuskanci zabe wanda nake da tabbacin cewa APC ce za ta lashe zaben 2023. Bisa irin mutanen da nake gani za su iya magance duk wata matsala da ta kunnu kai a cikin jam’iiyyar ta yadda har za ta iya cin zabe.
An kalubalanci kwamitin riko da Buni yake jagoranta bisa kara musu wa’adin shugabanci na jan ragamar harkokin jam’iyyar. Wasu sun kalubalanci kwamitin wajen barin tsirarun mutane musamman ma gwamnoni suna juya akalar jam’iyyar. Ko ka amince da wannan ikirarin?
A duk lokacin da mutum ya kasance a matsayin shugabanci, babu yadda za a yi ka gamsar da mutum miliyan 41. Dole ne ya kasance kana iya magance matsaloli da suke bijirowa wanda shi zai sa ka samu nasara. Shugaban kasa wanda ya kasance uba a cikin jam’iyyar ya yi gargadi wanda ya haifar da gagaruwar sauyi na gaggawa har ta kai ga an saka ranar gudanar da babban taron jam’iyya. Shugabanci yana da bukatar sauraron mutane tare da kokarin yin gyara. Idan aka zargi cewa ana gudanar da abubuwa wanda ba daidai ba ko juya akalar jam’iyya, a yanzu an gyara wannan domin masu rinjaye ne suka saka lokacin gudanar da babban taron jam’iyyar da kuma yadda jaddawalin zai kasance. Haka muka yi tsammanin zai faru. Idan aka yi maganar jan akalar jam’iyyar ya kasance ne tun kafin gargadin shugaban kasa. Amma a halin yanzu dai, abubuwa sun sauya kuma jam’iyyar tana samun ci gaba.