Luis Suares Zai Iya Lashe Kyautar Mafi Zura Kwallaye A Laliga – Simeone

Suares

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Diego Simeone, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar na gaba, Luis Suares, zai iya zama dan wasan da yafi yawan zura kwallaye a raga a kakar wasa ta bana da ake bugawa.

Luis Suarez ya ci kwallo 14 a wasanni 16 da ya buga a gasar La Liga, ya yin da za a shiga karawar mako na 22 daga ranar Juma’a kuma dan kasar Uruguay din ya yi wannan bajintar a Atletico Madrid a karon farko tun bayan rawar da Radamel Falcao ya taka.

‘Yan wasan Atletico da suka ci kwallo irin wanda Suarez ya zura a raga a bana sun hada da Christian Vieri a kakar wasa ta 1997 zuwa 1998 sai dai kafin shi akwai dan wasa Pruden da ya yi wannan kwazon a kakar wasa ta shekarar 1940 da kuma Baltazar da ya yi hakan a shekarar 1980.

Kuma dukkan ‘yan wasan ukun na Atletico Madrid su ne suka lashe kyautar takalmin zinare a Spaniya a matakin wadanda suka fi cin kwallaye a raga a kakar hakan yasa Simeone yake ganin wannan shekarar ma Suares zai iya kafa irin wancan tarihin.

Suarez ne kan gaba a cin kwallo a gasar La Liga a bana, idan ya lashe takalmin zinare zai zama dan kwallon Atletico Madrid na farko da ya yi hakan tun bayan Diego Forlan a shekarar bayan ya koma kungiyar daga Villareal 2009.

Sai dai kuma akwai wasu ‘yan wasan da ke takarar lashe takalmin zinare da suka hada da dan wasan Barcelona kuma kaftin din kungiyar, Lionel Messi da Youssef En-Nesyri da Gerard Moreno da kuma Karim Benzema.

Kwallo 14 da Suarez ya ci wa Atletico Madrid a La Liga sun hada da biyar da ya ci da kafar hagu da hudu da kafar dama da biyu da ka da kuma wasu biyun a bugun daga kai sai mai tsaron raga da daya a bugun tazara.

Suarez ya koma Atletico Madrid daga kungiyar Barcelona a karshen watan Satumbar shekarar data gabata, kuma a dan karamin lokaci ya zazzaga kwallaye a raga da Falcao ne ya taba yi wa kungiyar irin wannan bajintar.

Falcao dan kasar Colombia ya taimakawa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta lashe gasar Europa League da kuma UEFA Super Cup a shekarar 2012 da kuma Copa del Rey shekara daya tsakanin.

 

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Ligar bana:

Luis Suarez Atletico Madrid 14

Youseff En-Nesyri Sebilla 12

Lionel Messi Barcelona 12

Gerard Moreno Billarreal 10

Karim Benzema Real Madrid 10

Exit mobile version