Abba Ibrahim Wada" />

Lukaku Ya Amince Da Komawa Inter Milan

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Rumelu Lukaku ya amince da komawa kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan bayan ya amince da albashin da kungiyar zata dinga biyansa a duk shekara.

Tun kafin Antonio Conte ya zama kociyan na Inter Milan ya bayyana cewa yana son koyar da dan wasa Lukaku wanda ya zura kwallaye 15 a Manchester United a kakar wasan da ta gabata kuma kungiyar ta kare kakar a mataki na shida a kan teburin gasar firimiya.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana Inter Milan da Lukaku sun amince da juna sai dai har yanzu kungiyoyin biyu basu cimma yarjejeniya ba akan farashin dan wasan wanda Manchester United take neman a biya kusan fam miliyan 70

A satin nan ne dai Lukaku ya bayyana cewa Manchester United ce take da alhakin sanin kungiyar da zai ci gaba da bugawa wasa a kakar wasa mai zuwa sai dai alamu sun nuna cewa kociyan kungiyar ya bayyana wa dan wasan cewa baya cikin ‘yan wasan da zai yi amfani da su a kakar wasa mai zuwa.

Manchester United dai ta siyo Lukaku ne dai daga kungiyar kwallon kafa ta Evertion akan kudi fam miliyan 75 a shekara ta 2017 kuma tun bayan komawarsa kungiyar ya zura kwallaye 42 cikin wasanni 96 daya bugawa a kungiyar wadda ta lashe kofin firimiya sau 20 a tarihi.

Lukaku wanda tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Anderletch ne ta kasar Belgium ya taba bugawa Chelsea a wasa kuma a kwanakin baya ya bayyana cewa watarana yana son buga wasa a kasar Italiya a gasar Siriya A.

Exit mobile version