Wani ma’aikacin asibitin gwamnatin jihar Kano, Malam Aminu Umar Kofar Mazugal, ya mayar da jaka mai ɗauke da dalar Amurka sama da Naira miliyan 40 ga mai ita a cibiyar Abubakar Imam Urology, da ke Kano.
Mai jakar kuɗaɗen Alhaji Ahmed Mohammed ne, wanda ya manta da ita a filin ajiye motoci na asibitin kusa da wani masallaci.
- Dubban Mutane Sun Halarci Taron Mata Network A Kano
- ‘Yansanda Sun Kama Takardun Kuɗi Jabu Fiye Da Naira Biliyan 129 A Kano
A cewar Mohammed, mai jakar ya zauna kusa da masallacin ne kafin ya tafi filin jirgi, inda ya manta da ita kuma aka yi sa a ma’aikacin asibitin Malam Aminu Umar, ya tsinta yayin da yake shara tare da abokan aikinsa wanda ya ajiye a wajensa har sai da mai ita ya dawo nema.
Umar ya bayyana cewa bayan kimanin awa daya da tsintar jakar, Alhaji Ahmed Mohammed, ya dawo cigiya daga bisani ya miƙa masa inda ya nuna jin daɗi kan gaskiyar Umar, tare da ba shi tukuicin kudi.
Sai dai Umar ya ƙi amincewa da tayin, amma ya zaɓi ya bayar da lambar wayarsa, inda shi kuwa Mohammed, ya yi alƙawarin tuntubar shi da zaran ya dawo daga kasar waje.
Babban Daraktan Asibitin, Dakta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da yabawa da kyawawan dabi’un Umar, kana ya bayyana cewa hukumomin asibitin sun miƙa sunan Umar, ga hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano don karrama shi.