Ma’aikatan Hukumar NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aiki

Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), a ranar Alhamis, ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.

Mataimakin shugaban kungiyar, Idzi Isua, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar lamarin a ranar Alhamis da rana.

Mista Isua ya ce kungiyar na neman a biya ta bashin kudin karin girma na shekarar 2018 da 2019 da mambobin nata ke bi da sauran alawus.

“Babban abin damuwa shi ne cewa ma’aikatan da aka karawa girma a shekarar 2020 nan ba da jimawa ba suma za su bi sahun Yajin aikin. ”inji shi.

Exit mobile version