Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, ta lura da rahoton da kwamitin kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) ya fitar, dangane da matakan da Sin ta dauka kan sashe na 232 na matakan harajin dake da nasaba da gorar ruwa da karafa da Amurka ta sanya.
Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, ma’aikatar tana nazarin rahoton kuma za ta kula da shi bisa ka’idojin kungiyar WTO.
Jami’in ya kara da cewa, tushen abin da ke haifar da wannan matsala, shi ne matakin kashin kai da na kariya da Amurka ta dauka. Yana mai cewa, matakan mayar da martani da Sin ta dauka ta yi su ne kamar yadda doka ta tanada, kuma matakai ne na halal na kiyaye hakki da moriyar kasar.
Jami’in ya ce, Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta soke matakan da ta dauka na sashe na 232 game da haraji kan gorar ruwa da karafa, wadanda suka saba wa ka’idojin WTO, ta kuma yi aiki tare da sauran mambobin kungiyar WTO, wajen kiyaye ka’idoji da tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban.(Ibrahim)