Connect with us

Uncategorized

Ma’aunin Siyasar Najeriya A 2019

Published

on

Wasikar tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo tana ci gaba da kara tada kura da daukar sabon salo a siyasar Najeriya a ya yin da wasu ke ganinta a matsayin barazana ko kuma neman kawo karshen mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Ita dai wannan wasika ta kasance daya daga cikin abubuwan da aka maida su wani batu da ake tattaunawa akan shi kusan kowadayaushe, sannan har gobe ana kara samun fassarorin wasu kalaman na tsohon shugaban kasa, a ya yin da kullin ake ganin martani daga bangarori da dama.

Obasanjo dai ya kwarai wajan bayyana ra’ayinsa idan ya hango wani abu a siyasar Najeriya ko za a saurareshi ko kuma ayi watsi na nashi ra’ayin, sai a fi yawan lokuta hasashen na shi kan zama gaskiya.

Abu na farko ya fara daukar hankali game da wnnan wasika da ake yi wa lakabi da wasika mai zafi shi ne yadda aka fara sayar sa kwafinta a babban birnin tarayya Abuka kasa da sa’o’I 24 da hudu da sakinta.

‘yan Najeriya dai sun zuba na mujiya su ji irin dirar mikiyar da za a yi wa tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo daga bangaran shugaban kasa da kuma magoya bayansa, ganin cewa yanzu Shugaba Buhari an yafe masa yin laifi saboda haka ya zama shafaffe da mai.

Haka kuma ‘yan Najeriya sun kwana da sanin cewa shugaba Obasanjo ba kanwar lasa ba ne saboda haka ba kowa bane zai iya fada masa kai tsaye ba, dole sai an yi tunani, saboda kasancewarsa tsohon ala kwan kwan ne mai wuyar tabawa.

Wasikar dai ta yi wa mafiya yawan ‘yan Najeriya dadi a wannan lokacin da ba kowa ba ne ke iya nuna shugaba Buhari da yatsa domin ya fada masa gaskiya kuma a zauna lafiya, amma Obasanjo ya sha ta dubu ya fadi abinda ke cikin sai dai rai ya yi halinsa,  sai dai wasu na gani ya haskawa yan siyasa makomarsu a  zaban shekarar 2019.

Abubuwan da cif Obasanjo ya bayyana a wasikar da ya aikewa fadar shugaban kasa ba su musanta abubuwa da dama ba,  inda har suka jinjina masa dangane da fadin gaskiyar da ya yi akan abinda yake ganin wannan gwamnatin mai ci yanzu ta yi, sai dai sun ki amincewa da shi a wasu fannoni da dama.

Jikin wasu ‘yan Najeriya ya yi sanyi da suka lura an dauki dogon lokaci ba su ji abinda suka yi tunani ba, wato martani daga ‘yan farfagandon fadar shugaban kasa, sai ma da aka ji suna kare kansu da sanyayyar murya wanda ta yi kana da ja da bayan rago ba tsoro ne ba.

Haka ita jam’iyyar ta APC ta ce shugaba Obasanjo yana da hakkin fadin ra’ayinsa a matsayinsa na dan kasa kuma uba wanda ake girmamawa, saboda haka ba su yi mamakin wannan wasika ta shi ba, haka kuma sun kalubalanci shawarar da Obasanjo ya bada na shugaba Buhari ya hakura da batun tsayawa takara a zaban 2019.

Jam’iyyar ta ce, akan wannan batun ana kokarin raba hankalin shugaban Muhammadu Buhari wanda yanzu ba abinda ke gabansa sai kokarin cika alkawarin da ya daukarwa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe a 2015, saboda haka maganar tsayawa takara sai nan gaba za aji matsayarsa.

Wannan wasika dai ta baiwa bangarori daban daban damar tufa albarkacin bakinsu, gamayyar kungiyoyin arewa suka fara nuna goyan baya ga wasikar da Cif Obasonjo ya aikewa shugaba Buhari inda suka nuna karara cewa lallai Buhari ya ga za a shugabanci Najeriya.

Shuagaban gamayyar kungiyar ya ce Obasanjo ya fadi gaskiya kuma wannan kungiya tana bayansa, saboda haka suna ganin ya kamata Buhari ya yi karatun ta nutsu ya yi abinda yake iya yi kafin zabe mai zuwa.

Wannan martani na gamayyar kungiyoyin arewa ya ba su wasu mamaki ganin cewa Buhari dan arewa ne, kuma a arewa ne yake da maosya da kuma goyan baya amma ga wasu daga arewa suna kwance masa zani a kasuwa ya abin yake ne?

Shattima Yarima ya ce game da shawarar da Obasanjo ya baiwa Buhari na kadda ya kara tsayawa takara, yace muna ganin Buhari yana da damar da zai sake tsayawa amma babu abinda hakan zai haifar sai kara koma baya ga arewa da kuma Najeriya  baki daya.

Masu fashin bakin siyasa na jin tsoron wannan wasika ta Obasanjo domin a cewarsu duk shugaban da Obasanjo ya sanyo gaba sai ya kwantar da shi, domin da zaran ya fadi abun game da shi, cikin ikon Allah sai abun ya tabbata kuma Buhari ba fin sauran shuwagabanni ya yi ba.

Manyan Dattawan arewa irin su Balarabe Musa da Tanko Yakasai sun bayyana cewa wannan wasika ta Obasanjo yana dauke da gaskiya sai dai shu’umanci da taurin kai irin na shugaba Buhari ba zai bar shi ya saurari abubuwan gaskiya da Obasanjo ya hango masa.

Ita jam’iyyar adawa ta PDP cewa ta yi Obasanjo ya fadi ra’ayinsa saura ya rage ga ‘yan Najeriya wadanda suke ganin ba ayin dai dai su fito su bayyana na su ra’ayin.

Sannan har gobe tana sa ran kwace mulki daga hannun jam’iyyar mai mulki wato APC sai dai acikin wannan wasika Cif Obasanjo ya yi bayani karara cewa wadannnan jam’iyyu ba za su iya fitar da Najeriya daga halin ni ‘ya su da ta shiga ba saboda haka akwai bukatar a samar da wata jam’iyya da za ta dauki ‘yan kasa zuwa tudun mun tsira.

Haka kuma wasu masu fashin bakin siyasa na ganin Cif Obasanjo yana kokarin gwara kan ‘yan siyasa ne domin anan gaban ya a gane makomar siyasar Najeriya tunda yanzu ta fada hannun ‘yan bani na iya, kuma har yanzu anan koka da shugabancinsu musamman a matakin tarayya.

Wani abu da ya kara tada hankalin magoya shugaba Muhammadu Buhari shi ne, sunan maida martani amma saboda jan bakin da fadar shugaban kasa ta yi yasa gwaiwarsu ta yi la’asar, amma duk da haka akwai wadanda ba su hakura ba kullin sunan nan suna bayyana matsayinsu akan Buhari inda suke da fatan cewa zai sake tsayawa takarar shugaban in kasar a shekara ta 2019.

Wani abin dariya da magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari suka rika yadawa shi ne, wata wasika da suke ikirarin cewa diyar Cif Obansanjo wato Iyabo  ta rubuta zuwa gare shi, da sunan wai martani ne ta mayarwa da mahaifinta saboda haka uba ya fadi ba nauyi.

Wasu kuwa tunaninsu akan wannan wasika shi ne akwai wata boyayyar manufa game da wannan wasika ta Obasanjo a irin wannan lokaci mai zafi, da kowa ke ganin an zi wajan da za a yi gudun yada kanin wani, sai dai ba a son wanda za a yada din ba.

Saboda haka da yawansu sun tafi cewa Obasanjo yana yin sharar fage ne ga wasu yaransa da suke da aniyar tsayawa takarar shugabancin kasar  nan a zaben 2019, saboda haka bari ya fara nuna inda siyara zata kada ya ragewa sauran jama’a su bi ko su kaucewa wannan manufa ta shi.

Wasu kuma sun yi ammanar cewa wannan tsohon baya magana haka kawai, akwai abinda ya sani wanda mafi yawan jama’a ba su sani ba, kuma babu wanda zai iya gaya maka cewa Cif Obasanjo bai san yadda siyasa Najeriya take tafiya ba.

To indai haka ne, Cif Obansajo ya gama na shi, ya riga ya nuna makomar siyasar Najeriya, cewar Buhari kadda ya tsaya takara a shekara ta 2019 hujja ce da ke cewa idan ya yi kuskuran tsayawa takara zai sha mamaki, domin haka ta faru ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda Obasanjo ya gargade shi da kadda ya tsaya takara ya yi kunnen kashi da wancan shawara ya kuma ga abinda ya fi mamaki.

Shakka babu mafiyawan ‘yan Najeriya sun yi farin ciki da hasashen wasikar Obasanjo saboda gajiya da sukayi da farfagandar siyasa da wani abu mai kama da rainin wayo wanda akullin ake yi wa ‘yan Najeriya na cewar su kara hakuri, yanzu kuma ance wai za a ba su mamaki a cikin wannan shekarar ta 2018.

Lallai akwai fatan cewa idan har shugaba Buhari bai ba ‘yan Najeriya mamaki ba, to shi akwai yi wowar su bashi mamaki a 2019, musamman yadda za a kaya tsakanin shugaba Buhari da kuma wannan wasika ta Obasanjo.

Sannan akwai tabbacin cewa idan har Buhari ya yi shakulatar bangaro da wadannan shawarwari da aka ba shi a bayyane tare da yin manuniya akan makomar siyasar Najeriya, to ta Malam bata wuce amin. Amma dai akwai kallo a shekarar 2019.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: