Rachel Keke, sabuwar ‘yar siyasa a Faransa, an ce ita ce irin ta ta farko mai aikin share-share a kasar da ta zama ‘yar majalisar dokoki.
A baya dai Misis Keke ta yi shuhura ne a wajen jagorantar yajin aiki da zanga-zanga a otal mafi dadewa a kasar Faransa, inda ta yi nasarar yakin neman karin albashi da kuma kyautata yanayin aiki.
Nasarar da ta samu dai wasu magoya bayanta suka fara yi mata lakabi da “Muryar marasa ‘yan ci”. Inji jaridar the nation.