Dan takarar kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar APC mai wakiltar Yobe ta Arewa a jihar Yobe, Hon. Bashir Sheriff Machina, ya yi barazanar shigar da kara kan zargin sauya sunansa da na shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a cikin jerin sunayen da jam’iyyar ta aike wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a ranar Juma’a.
Jam’iyyar APC da wasu ‘yan takarar sanata a fadin jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya (FCT) ne suka sanya sunan Lawan a cikin sunan da aka aike wa hukumar.
- Lawan Na Fuskantar Barazanar Rasa Kujerarsa Wanda Ya Maye Gurbinsa Ya Ki Janye Masa
- Abun Mamaki: Lawan ya Manta Da Wasikar Murabus Din Abaribe A Gida
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Machina ya tsaya takara a zaben fidda gwani na jihar Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben fiida gwani da INEC da hukumomin tsaro suka sanyawa hannu.
Amma Lawan, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar kuma ya sha kaye a hannun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai shiga zaben fidda gwani na takarar Sanata na jam’iyyar a yankin Yobe ta Arewa ba.
Sai dai APC ta rubuta wa INEC wasika, inda ta sanar da hukumar zaben cewa shugaban majalisar dattawa ne zai tsaya mata takarar kujerar sanatan Yobe ta Arewa, wadda Lawan ke wakilta a halin yanzu.
Machina ya mayar da martani ga wannan matakin na Jam’iyya a daren Juma’a, kuma ya sha alwashin garzaya kotu domin kalubalantar yunkurin kwace masa hakkinsa.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Machina ya roki jam’iyyar APC da ta gyara sunansa, inda ya ce ba shi da wani zabi da ya wuce ya nemi a yi masa shari’a idan aka maye gurbinsa da na Lawan.
Machina, ya shan alwashin ba zai ja da baya kan wannan kudurin ba, ya ce, “A cikin jerin sunayen da aka aika wa INEC, an gano ba sunana bane. Ban sani ba ko kuskure ne, sunana ba ya cikin jerin sunayen da aka ce za a gabatar a yau ga INEC. Don ni ne dan takarar da aka zaba na jam’iyyar APC ta shiyyar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa.
“Ni ne zababben dan takara; Ban janye wa kowa ba, kuma ba zan janye ba, domin a matsayin hakki na wannan yake, shi ne aikin da ‘yan jam’iyyarmu da wakilai suka ba ni. Don haka cire sunana cikin sirri, rashin bin tsarin demokradiyya ne.
“Insha Allahu zan dauki matakai, na farko ta hanyar tunatarwa da kuma kira ga jam’iyyata cewa idan har da gaske aka yi wannan mataki a gyara, musamman idan aka yi kuskure. A gaskiya muna neman gyara daga kwamitin ayyuka na jam’iyyarmu ta kasa a karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, cewa akwai wata matsala kuma muna bukatar a gyara.”