• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

by Adamu Ibrahim Malumfashi
2 months ago
in Ra'ayoyi
0
Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wasa-wasa dai Musulunci na dawowa gidansa wato Nijeriya ta Arewa ta hanyoyi iri-iri. Ba dai sai an nanata ba. Arewacin Nijeriya da ma sassa da dama a jamhuriyar Nijar da Gana har ya zawa Senegal sassa ne na Musulunci inda ƴan mulkin mallaka na Ingila da Faransa suka yi iyakar ƙoƙarin su rusa shi. Ya ƙi ya bace, duk da yake an yi masa rotse.

Tarihi ya bayyana yadda wata ƙungiyar musulmi daga Mali ta zo Kano a ƙarni na sha biyar ta zauna ta fasa wucewa zuwa aikin Hajjin da ta fito yi. Waɗannan mutane da ake kira Wangarawa suna cikin na farko-farko da suka yaɗa Musulunci a Kano. Shehin malamin tarihi M.A. Al Hajj wani mutumin Sudan ya yi rubutu a kansu a mujallar Kano Studies wadda Jami’ar Bayero ta riƙa bugawa tun tana Abdullahi Bayero College wato tana ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello Zaria. Zuwan Wangarawa muhimmi ne domin sun zo ne a matsayin ƙungiya wato da yawansu, ba irin zuwan shehin malami ƙwara ɗaya ba kamar babban malamin nan Al-Maghili Al Tilmisani wanda ya yaɗa musulunci a ƙasar. Sauran ƙasashen Hausa su ma sun amfana da gudummanwar malamai musamman larabawa wajen yaɗa musuluncin. Marigayi Farfesa Ahmad Kani Shehin tarihi ya ambaci wasu daga cikinsu da irin ayyukan da suka yi a ƙasar Katsina. Daga baya malamai ƴan gida su ma sun bayar da tasu gudummwar kamar Muhammad Ibn Muhammad Al-Katsinawi al-Fulani wanda ya rasu a Misira a shekarar 1741 kafin ma a haifi Shehu Usman Danfodiyo. Shi ne aka ce ya koyar da littafin Imam Malik- Muwaɗɗa a masallacin Manzon Allah SAW Madina.

  • Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Legas  Ya Koma APC Daga PDP
  • Ko Barcelona Ta Kama Hanyar Lashe Gasar Laliga Ta Bana?

Da tafiya ta yi tafiya sai ƙasar Hausa ta fara yi wa kanta kirari da kanta ta fuskar samar da malamai Hausawa. Duk wanda ya ji an ambaci Wali Ɗan Marina ai ya ji sunan Bahaushe. Bahaushen ma na tsakiyar birni. Duk da yake Turawa da ƴan barandarsu sun yi ƙoƙarin su nuna malamin ba wani malami ne na a–zo-a gani ba. Tarihi da rubuce-rubacen da Farfesa John O. Hunwick da Dr Bobboi suka fitar a ƴan shekarun nan sun nuna cewa Wali Dan Marina babban malami ne da aka yi a birnin Katsina, kuma ya yi rubuce-rubuce da Larabaci da Hausa masu ƙayatarwa. Sarkin musulmi Muhammad Bello wato ɗan Mujaddadi Usman wanda ya fara mulkin ɗaya daga cikin biyu na Daular Usmaniyya bayan jihadi ya jinjina masa. Ga irin abin da ya ce a game da shi a cikin littafinsa Infaq al Maysur. Ya kira shi Al-ustaz, mai haskakawa kuma hanyar saman ilmi. Ya kuma ambaci wasu rubuce-rubucensa.

Waƙar da Wali Dan Marina ya yi a shekarar 1659, wato yau shekara 366 ke nan wadda ya yaba wa Sarkin Katsina na lokacin ta tabbatar da cewa ashe tun kafin 1659 gararuwan ƙasar Hausa da shari’a suke mulkinsu. Waƙar ta yaba wa Sarkin ne domin ya sanya an kashe mutumin da ya yi iƙirarin cewa shi ne Annabi Isa. Da malaman gari suka gaya wa Sarki mutumin ya yi ridda sai mai martaba ya bayar da umurni aka yi masa hukuncin da ya dace da na yin ridda su kuma jama’ar gari hankalinsu ya kwanta suka daina ƙorafi.

Zuwan Turawan mulkin mallaka ne aka yi ta yi wa Musulunci bugun kawo-wuƙa. Turawa sun yi watsi da tsarin ilmin da suka iske. Sun rusa makarantu ta ruwan sanyi, sun wulaƙanta malamai da almajiransu. Har bayan da suka kafa irin nasu makarantun waɗanda bahaushe ya kira na ƙarya na giri da yaudara wato Boko, sai malamin da ke koyar da addinin Musulunci da Larabci ya zama shi ne abin ƙyama. Albashinsa dan tsito ne in an kwatanta shi da na mai koyar da lissafi ko Ingilishi, harshen da suka dauka shi ne harshen manzanni. Kusan duk wata hukuma ta Musulunci sai da Turawa suka lalata ta suka ƙirƙiro tasu. A yau ba ƙarƙashen mulkin mallaka muke ba. Tun shekarar 1959 Lardin Arewa ya samu ‘yancinsa. Tun 1960 aka ba Nijeriya cin gashin kanta. Saboda haka idan har jihohin Arewa sun ce sun bayar da hutu domin ɗalibai da malamansu su yi azumi cikin natsuwa to, ina yin haka ya saɓa wa cin gashin kan? Ko gashin kan na nufin a gasa wani ya ci? Mun yaba wa Gwamnan jihar Bauchi da ya bi sahun ‘yanuwansa gwamnonin Kano da Katsina da Kebbi da ma waɗanda ban ambata ba a kan bada hutu domin azumi. Azumi wani abu ne mai muhimmanci a rayuwar musulmi. Soki burutsun da kungiyar kiristoci da wani ɗan amshinsu wai shi sakataren yaɗa labaran kungiyar ɗalibai suke yi duk shure-shure ne na ganin guguwar Musulunci da ta taso. Idan zan tambayi ƙungiyar Kiristoci da ta ce wasu ƙasashen larabawa irin su U.A.E da Kuwait ba su ba da hutu domin azumi, wannan ya isa hujja kada a bayar a duk wata jiha ta musulmi? Idan ma duk Larabawa sun ce ba su ƙara yin azumi ko salla ko ma in ɗebo ta da fadi, su ce ba su ba addinin, sai Hausawa su ce su ma sun bar addinin? Musulunci ba addinin Larabawa ne ba. Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam ba Annabin Larabawa ne ba. Annabi ne ga duk duniya har da shugabannin ƙungiyoyin wasu addinai da za su gane. Annabi Muhammad (SAW) rahama ne ga dukkan ‘yan Adam. Azumi ginshiƙi ne a tsarin Musulunci. Duk wanda ya ƙi yin sa, ya yi wa kansa sakiyar-da–babu–ruwa. Banda ɗauke nauyin zuwa makaranta to akwai wani abu ma da masu azumin ke buƙata. Ƙasa ta bushe tun ma a cikin damina. A yayyafa wa talakawa ruwa su ji daɗin yin tarawihi. Da ruwan ciki ake jan na rijiya. Mayunwaci bai iya daɗewa a salla.

Labarai Masu Nasaba

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

Bari ma in yi waiwaye. In yi bi-ta-da-ƙulli. Da jihohin Arewa na musulmi suke yin hutun lahadi ba su zuwa aiki to don su je gidan uban wane ne? A Katsina dai wannan ba zagi ne ba. A maye gurbinsa da hutun Juma’a ranar zuwa sallar Juma’a. Ranar Idi ce. Da ake yin hutu lokacin kirsimati ko wata Ista shi kuma hutun menene ne? Har yanzu Turawan na nan ne? Idan aka ce a yi hutu lokacin da yara ke taya iyayensu aiki a gona za su gane hikimar wannan tunda abinci zai zo gida. Lokaci ya yi da musulmi za su nuna wa duk wani mai shishshigi da takalar faɗa yatsa. Tsarin dimokuraɗiyya tsari ne na masu rinjaye a majalisa, su yi doka ta dace da mutane ma fi rinjaye. Ko musulmin Abiya ko Kuros Ribas sun nemi a ba ƴaƴansu hutu domin azumi?

A yi amfani da hutun a yi karatu, karatun ilmi na haƙiƙa. Da ‘yan bokon da ke mulki sun je makarantar Ramadan sun sauke kamar yadda suka je sakandare suka gama, wasu ma har sun je jami’a da ba su zama ɓarayi a ofis ba.

Da ba a riƙa tallata su a talabijin sun yi laya da biliyoyi ba. Da ba mu ga uba da dansa ba a gaban alkali ana cewa ku ɓarayi ne suna musu har lauyoyinsu na shedar zur. A sha ruwa lafiya.

Adamu Ibrahim Malumfashi, ya rubuta daga Jami’ar ABU Zaria


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AzumiDalibaiHutukanoKatsinaKebbiMakaranta
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnatin Kano Ta Umarci Ma’aikatanta Da Su Tantance Allbashin Watan Maris Kafin A Biya Su

Next Post

Sin Ta Kaddamar Da Sabon Shiri Kan Tsare-tsaren Musamman Don Bunkasa Sayayya

Related

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

6 months ago
Nijeriya
Ra'ayoyi

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

7 months ago
Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya
Ra'ayoyi

Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya

7 months ago
Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
Ra'ayoyi

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano

7 months ago
Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai
Ra'ayoyi

Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai

8 months ago
Azumi
Ra'ayoyi

Matsalar Kifewar Kwale-kwale A Jihar Jigawa

9 months ago
Next Post
Sin Ta Kaddamar Da Sabon Shiri Kan Tsare-tsaren Musamman Don Bunkasa Sayayya

Sin Ta Kaddamar Da Sabon Shiri Kan Tsare-tsaren Musamman Don Bunkasa Sayayya

LABARAI MASU NASABA

Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

May 8, 2025
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

May 8, 2025
Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

May 8, 2025
Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani

Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani

May 8, 2025
Waiwaye Game Da Gudummawar Shawarar BRI Ga Duniya

Waiwaye Game Da Gudummawar Shawarar BRI Ga Duniya

May 8, 2025
Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?

Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?

May 8, 2025
Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki

Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki

May 8, 2025
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

May 8, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

May 8, 2025
An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet

An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet

May 8, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.