‘Mafita Game Da Cutar Kwarona Da Ta Addabi Duniya’

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.

 

Annoba dai daga Allah take, za ta iya faruwa a matsayin jarabawa daga Allah da ya  kan jarrabci bayinsa ta inda ya so, wani lokaci sakamakon laifin bayinsa/ wani lokaci kuma jarrabawa takan zo a dalilin kusancin bayin Allah da Allah ba tare da laifi ba sai domin ya jarrabta imaninsu. Idan Allah ya kawo annobar sai ya sa ta zama alkairi ga muminai bayin Allah. Watao ba domin addu’ar Manzo Allah (s.a.w) da addu’ar mutanen kirki daga cikinmu ba, to da an kifar da mutanen wannan zamani. Domin wannan zamani shi ne, mafi muni da kazanta da babu abin da bama aikatawa. Mutane  suna fito na fito da Ubangiji.

Mutanen Annabi Musa kin biyayya kadai suka yi wa Allah ya kawo masifar da ta kifar da su.

Mutanen Annabi Lud (A.s) luwadi ne kawai aikinsu Allah ya kifar da su. Luwadi da madigo ya zama ruwan dare a wannan zamani. Kasha-kashen rayukan da ba su ji ba ba su gani ba. Bin umarnin bokaye da sunan malamai domin biyan wata bukata ta rayuwar da babu tabbas a cikinta. Hassada ta yi yawa, mugunta ta yi yawa, kiyyaya ta yi yawa, sharri ya yi yawa. Zina ta zama ba abin kunya ba, ba ma boye ta sai ga wanda yake da sauran ‘yar kunya, matan aure suna bin maza, maza su dinga bin matar aure a wannan lokaci da yake kurarre. Amana ta yi karanci. Makwabci ya bi makwbcinsa da sharri, mallami ya cutar da dalibinsa.

‘Dan’uwa ya bi dan’uwansa da sharri, aboki ba ya fatan alkairi ga abokinsa, jarirai ba su tsira ba a wannan zamani, uba ya yi zina da ‘ya’yan cikinsa, da ya yi zina da ‘yar’uwarsa da mahaifiyarsa domin jindadin kansa, ko dan biyan wata bukata ta duniya da take rayuwa ce kalilan mai yankewa. Wani ya cutar da wani ba tare da dalili ba.

A wannan zamanin ne mafi yawan mutane ba ma yi wa junanmu fatan alkairi sai sharri. Cutar da maraya da danne na kasanmu. Wannnan zamani ne da riya ta yawaita mu kan yi kokarin nuna wa duniya abin da ba ma kokarin aikata shi domin Allah. Muna biyyaya da fiffiko ga wanin Allah a kan Allah. Karya laifi ne da ba mu dauke shi a bakin ko mai ba. Tausayi ya yi karanci a zukatanmu. Muna nuna tsiraici da sunnan wayewa. Iyaye sun koma su ne yara, yara sun koma kamar iyaye ga iyayensu. Zamani ne da na sama baya duba na kasan shi. Mawadaci bai duban matalauci.

Wadannan su ne kadan daga abin da ya bayyana ya zama ruwan dare da ke faruwa a wannan zamani, wasu abubuwan ma ba su zo kunnuwanmu da mun sha mamaki.

Mafita shi ne, mu koma ga Allah, mu ji tsoron Allah, mu kiyaye Allah shi ne kadai mafita da zamu  rayu cikin aminci da kwanciyar hankali. Mutuna cewa, kowane sakan raguwa muke yi sannan muna kara kusantar kabari. Wannan rayuwa ta yi kadan ga ba wa maihankali da ya dinga aikata abin da ya ga dama, domin an yi wasu kafinmu, an yi wasu tare da mu kuma a yau duka duniyar takare musu. Mu sani cewa, Allah sai ya ga dama yake barinmu.

Rayuwa ribarta biyu ce, ka yi abin da zai amfani rayuwarka ta duniya ba tare da ka saba wa Allah ko ka cutar da wani ba, ko kuma ka yi abin da za ka amfana a lahirarka shi ne ka ci riba.

Mutuba, mugyara halayenmu domin addu’a ba za ta yi tasiri ba sai mun gyara halayenmu.

 

Allah ya ba mu mafita, ya shiyar da mu, ya yafe mana laifufukanmu, ya kawo mana karshen duk wata fitina

 

Sako Daga Anti Zainab Mohammed, Zariya.

 

 

“Jinjina Ga Nasiru El-rufa’i”

 

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, muna kara jinjina wa gidan jarida LEADERSHIP A YAU da suke kara ba mu dama don mu fadi ra’ayinmu, Allah ya kara muku basira da daukaka, ya kuma kare ku.

Hakika gwamna Nasiru El-rufa’i shi ne wanda ya fifita aikin hankali kuma ya bayyana wa duniya, ya tashi tsaye yayin da ilahirin dattawan Arewa suka zabi su kasance a zaune, ya je yayi abin da ya dace bayan wani ya yi abin da bai dace ba.

A shekarar da ta gabata, na yi rubutu a kan tataburza da ke tsakanin Gwamnan Jihar Kano da mai martaba Sarki Sanusi Lamido Sanusi II. Na yi hasashen faruwan abu irin wannan saboda dukkan alamu sun nuna. Mafi munin rigimar tube Sarki Sanusi shi ne, wulakancin da ya biyo baya. Tun daga cin mutunci da hadiman gwamna Ganduje suka yi wa Sarki Sanusi har zuwa ga tsare shi da hukumomin tsaro suka yi ba bisa ka’ida ba. Wadanda suka wulakanta Sarki Sanusi za su gani a kwaryar tuwonsu. Saboda yanda abun yake shi ne, kamar yadda ka shuka haka za ka girbe. Kamar yanda ka yi, haka za a yi maka duk girman kumatunka, duk yawan tarin naman wuyarka.

Gwamna El-rufa’i ya tabbatar wa duniya ba duka dattawan Arewa ne suke tsoron aiki da hankalinsu a lokacin da marasa hangen nesa suke kwamacala ba. Da farko El-rufa’i ya yi iya kokarinsa don ganin irin wannan fitina ba ta afku a jihar Kano ba. Daga lokacin da aka sanar da tsige Sarki Sanusi Lamido Sanusi II, gwamna El-rufa’i nan take ya sanar da ba sa mukami a Jihar Kaduna.

 

El-rufa’i bai tsaya nan ba, sai da ya biyo Sarki Sanusi har karamar hukumar Awe ta Jihar Nasarawa. Kazalika bai bar Jihar Nasarrawa ba sai tare da Sarki Sanusi.

A cikin al’umma da take da hangen nesa, mutane irin Sarki Sanusi Lamido tayin shugabanci ake yi musu kuma a tilasta musu shugabancin saboda kaifin basira da dumbin ilimi da Allah ya ba su. Amma kash, mu mutane ne masu karrama wanda bidiyon sa ya bayyana yana karban cin hanci, sannan kuma mu tsige wanda ya ce a yi gyara.

 

Sako Daga Mahmud Isa, Yola

 

08106792663

 

“Kira Ga Jama’ar Jihar Katsina”

 

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya.

 

Editan jaridar LEADERSHIP A YAU JUMMA’A, ina so ka ba ni dama in yi kira ga jama’ar Jihar Katsina da su bi dokar da gwamnati ta sanya na takaita zirga-zirga da kuma taruka, domin kauce wa wannan cutar watau choronerbirus. Mu ci gaba da addua da kuma bin dokokin da likitoci ke bayarwa. Allah Ubangiji ya kawo mana sauki, amin.

Sako Daga Saminu Mayentea, Batsari.

08166016029

 

 

Exit mobile version