Taron kasashe 16 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya na yaki da kwararar hamada (UNCCD) a birnin Riyadh ya zo a daidai lokacin da kwararar hamada ke ci gaba da yin barazana ga muhalli, da tattalin arziki, da rayuwar sama da mutane biliyan biyu a duniya. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, tattalin arzikin duniya na asarar kusan dala biliyan 400 a duk shekara a dalilin lalacewar kasa. Kana sauyin yanayi yana kara ta’azzara matsalar, tare da tsananin zafi, da tsawon lokaci na fari da rashin ruwan sama da ke kara haifar da asarar filayen noma. A cikin wannan halin kaka-nika-yi, babban nasarar da kasar Sin ta samu wajen yaki da kwararar hamada ta zama abin koyi ga duniya.
Kasar Sin wadda a tarihi tana daya daga cikin kasashen da kwararar hamada ta yi wa illa, ta sake sauya al’amura ta hanyar jajircewa, da aiwatar da manufofin kimiyya da ayyukan da suka dace. Jigon wannan sauyin shi ne aikin inganta muhalli na yankuna uku na arewaci wato “Three-North Shelterbelt Project” a arewa maso gabashin kasar Sin, wanda aka fi sani da babban koren ganuwa ko “Green Great Wall.”
- Gwamnan Zamfara Ya Rantsar Da Sabon Kwamishina Tare Da Yin Garambawul Ga Muƙarrabansa
- Ba Za A Bar Kowace Kasa A Baya Ba A Kokarinsu Na Zamanintar Da Kansu
Aikin wanda aka kaddamar a shekarar 1978, ya shafe fiye da murabba’in kilomita miliyan 4.9 na fadin yankunan arewaci, wato yankunan da suka taba yin fama da guguwar yashi da kuma kwararar hamada. Amma a cikin shekaru da suka gabata, an yi nasarar daidaita fiye da hekta miliyan 6.6 na yankin da ya lalace da daidaita gefunan manyan hamada, da kuma rage tashin guguwar yashi mai tsananin a arewacin kasar Sin, yanzu wandannan yankuna suna cikin kwanciyar hankali da ni’ima.
Yakin da kasar Sin ke yi da kwararar hamada ya tabbatar da cewa, kawar da gurbacewar kasa ba wai kawai aiki mai yiwuwa ba ne, har ma da kawo sauyi. Dole ne al’ummar duniya su yi aiki cikin gaggawa da hadin kai domin shawo kan wannan matsalar. Taken taron na UNCCD na bana, wani abin tunatarwa ne mai karfi cewa makomar busassun yankunan duniyarmu na da nasaba da makomar bil Adama. Kuma ta hanyar yin koyi da kasar Sin, da kuma himmatuwa wajen daukar matakan da suka dace, za mu iya tabbatar da cewa an kiyaye kasarmu daga kwararar hamada da makomarmu ga zuri’armu. (Mohammed Yahaya)