Wani mutum dan shekara 40 mai suna Nuhu Umar Usman, ya harbe matarsa ta biyu mai suna Ladi Nuhu, a kauyen Dangarfa da ke karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wanda ake zargin.
- Na Gama Aikina A Turai, Cewar Ronaldo
- Rundunar ‘Yansanda Ta Cafke Mutane 61 Da Ake Zargi Da Bangar Siyasa A Kano
Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya kwana a dakin matarsa. Wanda ake zargin yana da mata biyu da ‘ya’ya shida.
“An samu sabani a tsakanin matar da mijin, har babban dansa ya yi wa uban tsane shi kuma ya yi barazanar cutar da shi. Kafin faruwar wannan lamari, babban dan ya yi wa uban barazana.
“Wannan sabani ya sa mahaifin ya tanadi bindigarsa da shirin harbin duk wanda ya kutsa kai cikin gidan.”
Wakil ya ce bincike ya nuna cewa a ranar 28 ga watan Disamba, 2022, da misalin karfe 2 na dare, yayin da Usman ke kwance a daki daya shi da matarsa, ta fita daga dakin domin ta zagaya bandaki.
“A kan hanyarta ta dawowa daki, mijin ya farka bayan ya ji motsi kusa da dakinsa, kai tsaye ya dirka mata harsashi a ciki.
“Saboda haka, ta samu raunuka. An garzaya da ita zuwa babban asibitin Burra, amma likita ya tabbatar da rasuwarta,” in ji kakakin.
Wakil ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, CP Aminu Alhassan, ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu idan an kammala bincike.