Dan wasan bayan Manchester United, Harry Maguire, ya bayyana cewa yana tattaunawa da wakilansa kan yiwuwar tsawaita zamansa a kungiyar, duk da cewa bai yanke shawara ba tukuna.
Kwantiragin Maguire na yanzu zai kare a karshen wannan kakar wasa, amma Manchester United na da zabin kara masa shekara guda har zuwa 2026.
A shekarar 2023, Maguire ya yi kokarin komawa West Ham, amma hakan bai samu ba.
A yanzu kuma kungiyar ta dauko sabbin ‘yan wasa kamar Leny Yoro da Mathis De Ligt.
Bayan rawar gani da ya taka a wasan da suka doke Manchester City 2-1 a ranar Lahadi, Maguire mai shekaru 31 ya nuna sha’awarsa ci gaba da zama a Manchester United.
Da aka tambaye shi kan ci gaban tattaunawa, Maguire ya ce yana sa ran samun matsaya nan ba da jimawa ba, domin a cewarsa Manchester United gida ne a wajensa.