Mahajjata sama da miliyan biyu daga sassa daban-daban na duniya ne da suka isa masarautar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana, sun yi dafifi a filin Arafah domin gudanar da ibada muhimmiya.
Alhazan dai tun daga wayewar garin ranar Talata suka fara tafiya Muna daga Makkah zuwa Arafah, Muzdalifah da komawa Muna, hakan ya nuna an fara aikin Hajjin.
- Matawalle Bai Saci Kudin Jihar Zamfara Ba — Anas Kaura
- Za Mu Kawar Da Matsalar Tsaro A Nijeriya -Nuhu Ribadu
Ana sa ran mahajjata za su kasance a filin Arafah a yau, daga bayan Sallar La’asar da La’asar zuwa faduwar rana, suna neman gafarar Allah, Rahma, Albarka, shiriya, aminci, kwanciyar hankali, ci gaba da sauran addu’o’i.
Ana sa ran Malamai za su jagoranci mahajjatan Nijeriya wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaba da ci gaban al’ummar Nijeriya da kuma kasar ta shawo kan dukkan kalubalen da ta ke fuskanta ta fuskar tsaro da siyasa da tattalin arziki.
Bayan faduwar rana alhazai za su tashi zuwa Muzdalifah inda ake sa ran za su kwana kafin su koma Muna bayan an idar da sallar Asubah, domin jifan shaidan.
A gefe guda kuwa, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta nuna rashin gamsuwarta kan rashin isassun tantuna ga mahajjatan Nijeriya a Muna da Kamfanin Saudiyya ke da alhakin samarwa da isassun tantuna a Mashã’ir ga ‘yan Nijeriya.
Shugaban Hukumar Alhaji Zikrullah Kunle Hassan wanda ya gabatar da tambayoyi daga manema labarai a Muna kan halin da ake ciki, shi ma bai ji dadin shirin ciyarwar ba, wanda ya ce abincin bai wadatar ba.
Ya ce hukumar ta NAHCON ta yi hasashen cewa wannan matsala ta fi faruwa ne don haka ta ba da shawarar a shiga cikin lamarin, amma hukumomin Saudiyya da abin ya shafa sun dage cewa suna da babban dakin girki, da sanin makamar aiki da kuma wasu tsare-tsare guda uku na daban da za su gamsar da kowa.
Shugaban ya bayyana cewa tuni hukumarsa ta sanar da ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya kan halin da Nijeriya ke ciki dangane da tantuna da ciyarwa, inda ya ce an shirya za su hadu da daddare don duba halin da ake ciki a kasar tare da nemo mafita.
Tuni dai Alhazai suka ci gaba da gabatar da ibada da addu’o’i a filin Arfa.