Musa Muhammad" />

MAHANGA: Rikicin Manoma Da Makiyaya: Ya Kamata A Yi Hattara!

Tare da Musa Muhammad 08148507210   mahawayi2013@gmail.com

A duk lokacin da aka ce an samu wani rikici tsakanii wasu al’ummu, musamman na kabilanci ko na bambancin addini, to akwai matukar bukatar a yi hattara wajen daukar matakin magance shi, musamman idan matakin da za a dauka din nan daga Hukumomi ne, domin ita Hukuma ta kowa da kowa ce, kar ta sake ta dauki wani matakin da wani zai ga tamkar ta goyi bayan abokin fadarsa ne.

Ya na zama wajibi kuma ga ita Hukuma din ta dauki matakan da suka wajaba wajen dakile irin wadannan fitintinu, domin daya daga cikin hakkokin al’umma da ya hau kanta, shi karewa, tare da kulawa da rayuka da dukiyar al’umma. Don haka tilas ne idan ta ga ana irin wadannan fitintinu ta dauki matakan da za su kawo karshensu.

Toamma, kamar yadda na fada, akwai bukatar ganin an dauki matakin da zai zama bai-daya, wanda zai zama an kafa dokar da za ta shafi kowa da kowa, ba wai dokar da za ta kasance tamkar an dora wa wani bangare ne kawai ba.

Na yi wannan shimfida ne bisa irin munanan rigingimun da ke faruwa a yanzu tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan, musamman a jihohin Arewa, inda maimakon Gwamnonin jihohin su dauki matakan da za a samu maslaha, amma sai ya zama suna daukar  matakan da za su kara jagula abubuwa.

Shi wannan rikici na makiyaya da manoma, rikici ne da ba yau aka fara shi ba, rikici ne da za a iya cewa ‘kunni ya girmi kaka,’ wato an dale ana yinsa, amma sai dai abin takaicin shi ne, ya fi kazanta a ’yan wadannan shekarun, kuma ma a wuraren da a da ba a samu. Wannan ne ya sa Gwamnonin wasu ke jihohin daukar matakan da za su kara dagula lamarin.

Ya na da muhimmanci a gane cewa wajibi ne makiyayi ya samu wurin da zai yi kiwon dabbobinsa, wanda saboda haka ne ya sa ba ya zama a cikin gari, kullum Ya na daji, domin darajar dabbobin ita darajarsa, kuma zai iya yin komai don ganin dabbobin nan nasa sun samu abinci.

Bayan ga zama daji da makiyayan ke yi, haka kuma ba sa iya zama waje daya, kullum suna yawo ne, yau suna nan, gobe suna can, don kawai su samar wa dabbobinsu abinci, wanda kuma ta hanyar haka ne ake samun matsala, yadda wasu lokuta dabbobin nasu kan bi ta gonar manomi su yi masa barna, daga nan kuma in ba hankali aka yi ba abin ya zama rigima.

Tun lokacin ina karami na san lokacin da ake samun irin wadannan matsaloli, har akwai lokacin da idan wasu Fulanin suka bi ta hanya domin zuwa rani, to mummunar barna suke yi wa manoma, wanda zan iya tunawa har kara ake kaiwa wajen Mai garinmu, ya sasanta a biya diyya. Amma wasu lokutan har abin ya kan kai ma zubar da jini.

To, irin wannan ne yake faruwa a yanzu, amma na yanzu sai ya zama ya zo da sabon abu, tamkar ba irinsa ne aka yi fama da shi a shekarun baya din ba, ta yadda har wasu Gwamnonin na kokaron mayar da makiyayan cikin rukunin ’yan ta’adda.

Don haka ne na ke ganin lallai ya kamata gwamnatin tarayya ta yi wani abu kan wannan lamari, musamman bisa la’akari da matakan da Gwamnonin jihohin Taraba da Benuwe suka dauka, wanda tamkar na haramta wa makiyayan kiwo ne a fadin jihohin nasu, irin matakin da Gwamna Fayose na jihar Ekiti ya dauka a shekarar da ta gabata, wanda kuma ya jawo babbar matsala.

Haka su ma wadannan Gwamnoni suka dauki wannan mataki, inda suka haramta wa makiyayan kiwo a jihohin nasu, wanda ya sa wasu gauga’un kauyawa suka dauki doka a hannuwansu suka auka wa Fulanin, inda aka tafka asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa, tare kuma da kashe wasu rayukan da ake zargin makiyayan ne suka ka yi.

Gudun jagulewar wadannan al’amura ne ya sa wasu manya a Arewacin kasar nan suka fito suna yin gyara ga wadannan matakai na gwamnatocin wadannan jihohi biyu, inda suka yi kira da cewa a bi komai a hankali, kasar nan ta kowa da kowa ce, kuma kowa na da ikon zama a duk inda yake so a duk fadin kasar nan.

Mai alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya fito ya mayar wa da wadannan Gwamanoni martani game da sanya Makiyayan a cikin ’yan ta’adda, inda ya bayYa na cewa su Fulani ba ’yan ta’adda ba ne. Ya na mai cewa babu inda kungiyar Fulani ta ce makiyayan su kashe jama’a. Inda dai kawai ya dura laifin duk wadannan kashe-kashe a kan hukumomi da jami’an tsaro.

Ya na mai cewa babu inda kungiyar Miyetti Allah ta ce Fulani su kashe jama’a haka suddan. Ya kuma bayYa na cewa wadannan rigingimu, ba wai fada ne tsakanin musulmi da kirista, ko tsakanin musulunci da kiristanci ba, ya ce abin da ke faruwa, rashin jituwa ce, wacce kuma ta ke ba bakuwa ba a tsakanin jama’a.

Shi ma Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Sanata mai wakiltar mazabar Sakkwato ta Tsakiya, Sanata Aliyu Magatarda Wamakko, ya bayYa na cewa Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom da takwaransa na Taraba, Darius Ishaku su ne ke da laifin duk kashe-kashen da ke gudana a jihohinsu, saboda abin da ya kira da rashin adalci irin nasu da rashin bin tsari a harkar da suke bi wajen aiwatar da dokar hana kiwo, wanda in ba hankali aka yi ba, wannan zai sa a kori wasu daga jihohinsu na haihuwa.

Sanatan ya ce, maimakon wadannan Gwamnoni su samar da hanyoyin da suka dace wajen shawo kan wannan matsala ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar, sai kawai suka bi son zuciyarsu, ta yadda suke kara jagula harkar, wajen samar da asarar rayuwa da dukiyar jama’a.

Sanata Wamakko ya bayYa na cewa wannan rikici tsakaninin manoma da makiyaya abu ne da aka kwashe shekara da shekaru ana yinsa, amma ya fi munana a ’yan shekaraun nan saboda karuwar jama’a da ake da su a duniya.

Daga nan sai Sanatan ya jawo hankalin Gwamnonin da cewa su kasance masu yi wa kowa adalci, domin tsarin mulkin kasar nan ya ba kowa damar ya zauna duk inda yake so a fadin kasar nan don neman halaliyarsa ba tare da wata tsangwama ba.

Sanatan ya kuma yi Allah-wadai da ’yan siyasa da kuma kafafen sadarwa na Soshiyal Midiya da ke zargin wai Fulani ne ke da laifi a wadannan fitintinu. Inda ya ce, ai su ma makiyayan ana kashesu a rugagensu, kuma ana yanke masu dabbobi.

Ya ce, matakan hana kiwo da Gwamnonin suka dauka shi ya kara cusa kiyayya da kyamar makiyayan, wanda ya sanya wasu kyauyawa daukar doka a hannunsu wajen kai wa Fulanin hare-hare don korarsu daga jihohin nasu.

Daga nan sai Sanatan ya yi kira da a gudanar da wani babban taro na kasa na masu ruwa da tsaki don shawo kan wannan matsala gaba daya.

Ya na mai cewa in gwamnatin tarayya ba ta shiga gaba don samun mafita game da wannan matsala ba, to wasu Gwamnonin za su ci gaba da sanya siyasa a harkar, kawai don amfaninsu na kashin kansu na siyasa, alhali wasu na can ana kashe su, tare da barnata masu dukiya.

Tare da fatan za a dauki wadannan shawarwari na wadannan manya, musamman yadda abin ya kasance da cewa shi Mai Alfarma Sarkin Musulmi, shi ne Shugaban amintattu na kungiyar Miyetti Allah. Tare da fatan za a samu masalaha a wannan mummunan abu da ke tunkarar al’ummarmu.

 

Exit mobile version