Mahara 5 Tare Da Sojoji 4 Ne Suka Mutu A Harin Jihar Yobe

Rundunar sojojin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar jami’in ta daya, sojoji uku a yunkurin harin da mayakan Boko Haram suka yi kokarin kai a ranar Asabar, a barikin sojoji da ke Buni Yadi, ta karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Sanarwar, wadda ta fito daga mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojoji, Kanal Sagir Musa, tare da tabbatar da halaka mayakan guda biyar a harin.
Sanarwar ta kara da cewa, “wanda a lokacin da maharan suka yiwa barikin sojojin tsinke a kokarin kai harin, a motocin yaki guda 4, da makami kirar ‘Mine Resistant Ambush Protection’ 1 da makamai makamantan su (MOWAC)”.
“Wanda a cikin wannan yanayi ne, mayakan suka fuskancin koma baya sosai wanda biyar daga cikin maharan suka halaka. Wanda muka samu bindigogi kirar AK 47, guda 9, da bindiga mai harbo jirgin sama guda daya (1d Anti Aircraft gun), gammon harsashen da ake amfani dashi wajen harbo jirgin sama 121 (12.7 mm Anti Aircraft ammunition), tare da mugganan makamai da dama, ciki har da abubuwa masu fashewa, da babur din hawa (Bajaj)”.
Ya kara da cewa, wanda kuma a cikin rashin sa’a, jami’in sojoji daya tare da sojoji uku sun kwanta dama a lokacin da suke fafatawa da maharan. Ya ce, sojoji 5 ne samu raunuka, wanda yanzu haka suke samun kulawar likitocin barikin.
“wanda a bisa ga wannan ne, babban Hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya yaba da kokarin da sojojin ke yi a yankin arewa maso-gabas dangane da nasarorin da suke samu a kan mayakan, a yan kwanakin nan. Ya bukaci su ci gaba da aiwatar da aikin su bisa kwarewa, a kokarin su na kare kasar su”. Inji shi.
“bisa haka ne kuma, rundunar sojojin Nijeriya ta yaba matuka dangane da wadanda suka kokari wajen bayar da bayanan da suka bayar da nasarar dakile yunkurin wadannan mahara, wadanda mayakan suka yi kokarin kaiwa barikin da ke garin Buni Yadi”.

Exit mobile version