Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu ya bayyana cewa ma-haukaci kadai ne zai iya sake zaben jam’iyyar APC duba da irin bakar wahalar da ‘yan Nijeriya suka shiga na tsawon shekaru takwas na mulkin APC.
Ayu ya bayyana hakan ne a Jihar Benuwai lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, inda ya bukaci mutane su zabi duka ‘yan takarar jam’iyyarsa.
Ya ce PDP ta magance matsalar gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, sannan suna kokarin lallashin fusatattun gwamnonin PDP guda biyar wadanda suka bijire.
Ya ce wannan shi ne dan takarar shugaban kasa daya tilo na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar wanda ya yi alkawarin idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai dawo da zaman lafiya a wannan jiha da kuma sake bude tashar jirgin kasa da ke jihar.
Haka kuma Ayu ya ce duk da cewa akwai korafe-korafe a cikin babbar jam’iyyar adawa, ya dage da cewa jam’iyyar ba ta rabu ba, yana mai jaddada cewa tuni jam’iyyar ta fara tattaunawa da dukkan ‘ya’yanta da suka fusata domin ganin sun dawo cikin jam’iyyar.
“Abin da dukkaninmu muka sani shi ne, ana shan wahala a kasar nan a cikin she-karu takwas da APC ta shafe a kan mulki, wanda ke da matsalar tabin hankali ne kwai zai sake zaben APC. Kar ku kuskura ku bata kuri’unku.
“Ku zabi kowane dan takarar PDP, jam’iyyar ba ta rabu ba. Akwai mambobi kali-lan da suka fusata kuma muna magana da su. Za mu tabbatar sun dawo cikin jam’iyyar domin mu yi aiki tare gaba daya. Mako daya ya isa a sauya komi. Dama hakan yana faruwa kuma ina tabbatar da cewa za mu karbi kowa da kowa,” in ji shi.
Ya roki gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya dawo domin yakin ceto Nijeri-ya daga hannun APC.
Ortom yana daga cikin mambobin gwamnonin PDP na G-5, tawagar fusatattun gwamnonin guda biyar na jam’iyyar wanda gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike yake jagoranta da ke neman sai Ayu ya sauka daga mukaminsa a matsayin sharad-in yin sulhu.
Sauran mambobin na G5 sun hada da gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwanyi da gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu da kuma gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.