Hukumar kula da abinci ta Duniya ta yi kira ga al’umma da su kula da mahimmancin yin amfani da abinci mai gina jiki saboda karin lafiya.
Ta ce, a sabuwar shekara ta 2021, yana da mahimmanci mutani su kula da yin amfani da abinci mai gina jiki, kamar su kankana da abarba da lemu da mangwaro da ayaba, saboda suna bai wa jiki lafiya da kuzari.
Hakama wajen abinci a yi amfani da Koko da Kukumba da sinadari abinci mai inganci domin karin lafiya da kuzari.
Ganyen alaiyahu da ya kuwa da kuka da manja mai inganci yana kara lafiya.
Shekarar 2021 shekara ce da ya kamata ayi yaki da cututtuka mai nakasa rayuwar dan Adam a tabbatar da ingan taciyar rayuwa.
Ta hanyar yin amfani da abinci mai gina jiki da kayan marmari da ganye mai amfani a jiki da man girki zamu iya gina rayuwa mai kyau namu dana yaranmu. Kuma ta haka zamu yaki cututtuka da ke addabar jikin dan’adam .
Kowani jiki yana bukatar samun abinci mai inganci saboda yana taimakawa ganganjiki. Wajen ginashi da samu lafiya.