Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a kasar Hausa da ke yammacin Afirka, wadda tarihi ya tabbatar da cewa tsohuwar masarauta ce da ta kafa shekaru aru-aru da suka gabata tun a zamanin jahiliyyar kafin zuwan addinin musulunci. Sannan kuma masarauta ce wadda ta taimaka wajen bunkasa garin Kano hadi da Arewa da
ma Najeriya baki daya.

Birnin Kano ya kasance babbar cibiyar kasuwanci a arewacin Nijeriya tare da sauran wasu kasashen makobta da nahiyar Afrika. Haka kuma masarauta ce mai matukar tasiri da karfin fada aji a nahiyar Afrika kana wadda ta taka muhimmiyar raw wajen habaka da bunkasa al’adun Hausawa hadi da harshen baki daya.

Bisa ga bayanan da masanan tarihi suka taskace, sun ce salin kalmar ‘Kano’ ya zo ne ta hanyar mutanen da suka fara zama a Kano, wadanda makera ne da suka zo daga garin Gaya wajen neman kasa mai arzikin tama, wadda ake sarrafa wa don yin karfe da ita. Wanda su ka yi dacen samun nau’in dutsen mai dauke da sinadarin tama, kuma waje mai albarkar kasar noma da ruwa da dazuukan da za a yi farauta.

Bugu da kari, daji ne mai wanda ya tattaro manyan duwatsu da tsaunuka wanda zai taimaka don samun mafakar da mutum zai buya daga mahara ko dabbobi masu lahani, wadanda suka hada da dutsen Dala da Goron Dutse, Fanisau tare da Jigirya da Magwan. Sannan baya ga wannan akwai koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da
suka hada da kogin Jakara, da na kogin Kano.

Wanda wannan ya bai wa jama’a daga sasaa daban-daban zuwa garin a lokuta da dama, wanda masana tarihin birnin sun ce daga cikin mutanen da suka fi shahara a cikin wadanda suka
fara zama a garin akwai wani jarumin mafarauci mai suna “KANO”, kuma ta sunansa ne garin Kano ya samu suna.

Daga cikin masana Tarihin Daular Kano, akwai Dakta Tijjani Muhammad Naniya ya ce har kawo yanzu masana ba su tantance lokacin da mutane su ka fara
zama a Kano ba.

Sannan a ya kara da cewa, masana ba su gama tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a Kano ba. Ya ce saboda akawai garuruwa masu sunan Gaya a Kano, Nijar da ta jihar Sakkwato.

A hannu guda kuma ya ce babu cikakken bayani dangane da lokacin da aka fara zama a Kano ba, amma an taba gano wata makera kusa da dutsen Dala wadda masana suka ce ta kai shekara 200 bayan Annabi Isa (As).

Dangane da wannan batu, masana sun yi hasashen cewa an kafa garin Kano yau kimanin shekaru 400 kafin zuwan addinin musulunci, wanda kiddidiga ta kiyasta birin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa.

A batu na daban kuma, masana sun ce a lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama’ar garin a karkashin mulkinsa, sun ce a wancan lokacin, jama’ar da suke zaune a kauyukan Dala, Goron Dutse
da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabancin mutane daban-daban, wanda sai daga baya ne, a lokacin da garuruwan suka bunkasa, sai dangantaka tsakaninsu ta kara inganta kuma aka samu shugaba daya wanda ya hada kan mutanen, shi ne Barbushe, wani shahararren mafarauci.

Sarakunan da suka fi shahara a Kano
1. Sarki Usmanu Zamnagawa, ya na daga cikin sarakunan Kano da suka
shahara saboda shi ne ya yi juyin mulki, ya kashe sarki lokacinsa, wanda ya batar da sarkin, ba a sake ganin sa ba, kuma ba a ga ko gawarsa ba. Wasu na tunanin cewa kila ya dafa gawar sarkin ne ya cinye, ko kuma ya haka rame ya binne shi, wanda saboda haka ne ake masa kinaya da: Zamna-gawa.
2. Sarki Yaji dan Tsamiya, ya na daga cikin sarakunan Kano wanda a zamaninsa ne sarakunan Kano suka fara karbar musulunci, sannan ya yi
kokari wajen tabbatar da ganin cewa musulunci ya zama addinin mutanen masarautar sa. Sannan kuma a lokacinsa ne Wangarawa daga Tambuktu a karkashin Shiekh Abdurrahman Az-zagaiti, daga kasar Mali suka shigo garin Kano kan hanyarsu ta tafiya aikin hajji.
3. Sarki Muhammadu Rumfa, wanda ya taso da gidan Sarki daga kusa da dutsen
Dala zuwa gidan Makama saboda cunkoso da aka fara samu a lokacin, sannan kuma shi ne ya assasa bai wa sarakunan tsaro. Haka kuma Sarki Rumfa ne ya gina gidan sarkin Kano na yanzu, kuma ya kawo sauye-sauye da dama a tsarin tafiyar da sarauta a Kano.
4. A jerin sarakunan Fulani kuma akwai Sarki Sulaimanu, wanda ya fuskanci kalubale sosai daga wajen malamai da suka karbo tuta, amma duk da
haka ya jagoranci Kano tare da jajircewa.
5. Ibrahim Dabo Ci-Gari, shi ne ya murkushe tawaye da dama, tare da samun nasarar cinye garuruwa, sannan tun daga lokacinsa ne ‘ya’yansa da
jikokinsa suke sarautar Kano.
6. Abdullahi Bayero ya na cikin jerin sarakunan Kano da suka yi shuhura saboda abubuwa da dama tare da
sauye-sauyen da ya jawo na zamani.
7. Sarkin Kano Mallam Sunusi na daya: shi ne sarki kuma malami wanda a lokacin shi ya taimaka wajen daidaita al’amurra a wannan babbar masarauta.
8. Ado Bayero shi ne ya fi kowane Sarki dadewa a karagar mulkin birnin Dabo, daga cikin sarakunan Fulani, kana kuma wanda ya yi tsayin daka domin kare martaba da mutuncin Kano, haka kuma ya yi zamani da gwamnoni 16.

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shi ne Sarki na 15 a jerin sarakunan Fulani wadanda suka yi sarauta a Daular Kano. An haifi Mai Martaba ranar 1 ga watan Yulin 1961 a Kano, wanda ya gaji mahaifin shi, Marigayi San-Kano, Dakta Alhaji Ado Bayero, biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka wajen nada shi a ranar 9 ga watan Maris na 2020, bayan sauke Sarkin Kano na 14 a Daular Fulani Muhammadu Sanusi na biyu a ranar 9 ga watan Maris 2020.
Mai Martaba Alhaji Ado Bayero ya yi sarautar Kano daga 1963 zuwa 2014, wanda ya rasu a ranar 6 ga watan
Yunin shekarar 2014.

Bugu da kari Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne na biyu a jerin ya’yan Alhaji Ado
Bayero, kuma ya fara da karatun alku’ani mai girma da na fikihu a nan cikin gidan
Sarki, wanda daga bisani ya yi Furamare a kofar Kudu sannan ya zarce zuwa Kwalejin gwamnati ta Birnin Kudu.

Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya kammala digirinsa na farko ne a kan aikin jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi aikin hidimar kasa na shekara guda a gidan Talabijin na Kasa NTA a Makurdi ta jihar Benue.

Har wala yau ya tafi makarantar koyon tukin jirgin sama ta
Flying College da ke Oakland a jihar Carlifonia ta kasar Amurka.

Haka zalika, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi aiki a matsayin jami’in hulda da jama’a na Kamfanin sufurin jiragen sama na Kabo Air, sannan daga bisani ya zama injiniya a sashen direbobin jirgin sama.

A 1990 ne Sarkin Kano, Alhaji Dakta Ado Bayero ya nada Aminu Ado Bayero a matsayin dan Majen Kano kuma
Hakimin Dala, kafin daga baya likkafa ta yi gaba inda aka nada shi dan Buram Kano a cikin watan Oktoban 1990.

A 1992 ne aka nada shi aTurakin Kano
sannan daga bisani a 2000 ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, kana kuma ya taba shugabancin kwmaitin shirya Hawan Daba na fadar Sarkin Kano.

A 2014 ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya nada shi a matsayin Wamban Kano, kuma Hakimin Birni. Wanda kuma a 2019 ne gwamnatin Jihar Kano ta nada Alhaji Aminu Bayero a matsayin Sarkin Bichi, kuma a ranar 9 ga
watan Maris shekarar 2020 ne gwamnatin Kano ta nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15 a Daular Fulani.

Exit mobile version