Majalisar wakilai na duba yiwuwar amincewa da dokar zabe wanda a ciki har da gudanar da zaben 2027 a cikin kwana daya.
Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, wanda ya bayar da wannan tabbacin, ya nuna cewa idan aka amince da matakin kuma shugaba kasa ya sanya hannu, za a iya gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a rana guda.
- An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi
- Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi
Abbas ya yi wannan magana ne ga wakilan Kungiyar Tarayyar Turai (EU) wadanda suka saka ido a zaben Nijeriya a 2023 a Abuja.
Tawagar da ke karkashin jagorancin, Barry Andrews ta kuma ziyarci hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda shugabanta, Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa jinkirin da ‘yan majalisa ke yi wajen gyaran dokar zabe ta 2022 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zabe a 2027.
Wakilan, wadanda suke Nijeriya tun kusan makonni uku domin nazarin matakin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahotonsu na bayan zaben 2023, sun kuma yi tattauna da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Abbas, a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Leke Bayeiwu, ya shaida wa tawagar EU cewa rahotanninta kan zabukan shekarar 2023 ana la’akari da su a cikin sauye-sauyen gyara dokar zabe da na dimokuradiyya da Majalisar dokoki ke gudanarwa.
Abbas ya ce, “Ina so in bayyana cewa shugabancin kasar nan karkashin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kokarin tabbatar da cewa mun inganta tsarin zabenmu, musamman game da abubuwan da masu saka ido na kasashen waje suka lura da su a lokacin zaben 2023.
“Mu a majalisar kasa ma mun kasance cikin aiki tukuru wajen tattara mafi yawan batutuwa da suka taso daga zaben 2023, domin mu ga yadda za mu iya magance su ta hanyar bin dokoki, domin zabenmu na gaba ya kasance mai inganci da amsuwa a idon duniya.”
Ya shaida wa tawagar cewa taron shugabannin majalisar dattawa da na majalisar wakilai da aka yi kwanan nan ya yanke shawarar warware batutuwan gyaran tsarin zabe cikin hanzari.
Ya bayyana cewa ra’ayin da yawa daga ‘yan majalisar kasa shi ne, gudanar da zabe a rana guda ba wai kawai zai kara inganci da gaskiya a gudanar da zaben kadai ba, har ma zai rage yawan kashe kudade na kusan kashi 40 cikin dari.
Ya ce, “Kamar gudanar da zabe a rana daya, wanda zai bayar da damar gudanar da zaben shugaban kasa da mambobin majalisar tarayya da gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisar dokoki na jihohi duka a rana guda.
“A tunaninmu, zai taimaka wajen rage kashe kudaden gudanar da zabenmu har kashi 40 cikin ddari idan muka iya gudanar da zabukan cikin rana guda. Hakan zai kuma inganta gaskiya da karfafa aiki yadda ya kamata, musamman wajen fitowar masu kada kuri’a.”














