Majalisar Dattawan ta karyata zargin da ake yi cewa shugabanninta sun karɓi cin hancin dala miliyan 10 don hana a tabbatar da nadin Abdullahi Ramat a matsayin shugaban Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC). Majalisar ta bayyana zargin a matsayin “ƙarya mai hatsari wadda ba ta da hujja ba.”
Tsohon hadimin mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, mai suna Alwan Hassan, ne ya yi iƙirarin cewa an bai wa shugabannin majalisar cin hanci don su daƙile tabbatar da naɗin Ramat. Sai dai a cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Sanata Yemi Adaramodu, ya fitar a daren Juma’a, ya ce wannan zargi “ba shi da hujja” kuma matakin majalisar ya samo asali ne daga “ƙorafe-ƙorafen jama’a da masu ruwa da tsaki.”
- Duk Matakin Ilimin Bokon Mutum Bai Kamata Ya Yi Wasa Da Sana’a Ba – Ramatu Bello
- Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba
A cewarsa, “Dakatar da tantancewar Ramat ya faru ne saboda ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma matsin lamba daga wasu ƙungiyoyin da ke adawa da naɗinsa. Wannan ba shi ne karo na farko da Majalisar Dattawa ke dakatar da wani ɗan takara saboda irin waɗannan dalilai ba.” Adaramodu ya kuma bayyana cewa Alwan Hassan “mutum ne da ya karɓi kwangilar ɓata suna,” yana mai gargaɗin cewa majalisar ba za ta lamunci sharrin siyasa ko ƙagaggen labari ba.
Sanatan ya ƙara da cewa Majalisar Dattawa za ta ɗauki matakin doka a kan Hassan don tilasta masa ya tabbatar da zargin nasa a bainar jama’a. “Ba za mu bari wani ya ɓata sunan majalisar da iƙirarin ƙarya ba. Za mu hadu da shi a kotu,” in ji shi.
A ƙarshe, majalisar ta sake jaddada ƙudirin na tabbatar da gaskiya da tsabta a dukkan tsarin tantancewa da tabbatar da muƙamai, tana mai cewa babu wani ɗan takara da za a tabbatar da shi ba tare da cikakken bincike da tabbatar da cancanta ba.














