Majalisar dattawa ta sake amince wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciwo wasu bashi da ya kai Dalar Amurka Biliyan 8.2, kwatankwacin Naira triliyan 7.5 domin lamuni na dogon zango.
Shugaban kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar dattawa, Mohammed Sani Musa, ya ce sun amince da wadannan bukatu na shugaban kasa ne bayan sun saurari ba’asi daga wurin jama’a.
- Masarautar Zazzau Za Ta Yi Nadin Sabon Magajin Gari
- Likita Ya Shiga Hannu Bayan Kashe Wata Da Allurar Zubar Da Ciki A Kano
Ya amincewa da tsarin zai zama wata hanya ce da za ta bada dama na amfani da na’urar zamani wajen gane abubuwa da yadda za a aiwatar da kudaden.
Kazalika, mataimakinsa, Mohammed Ali Ndume, ya yi karin haske cewa a cikin kasafin kudin na 2024 aka kawo wannan bukata kuma sun amince masa da wannan sauyi na mayar da kudaden asusun lamuni domin wannan shi ne kasafin kudin Shugaba Tinubu na farko, kuma ba sa so a ga kaman sun hana ruwa gudu, saboda haka za su tabbatar da sa ido a yadda wannan tsari zai tabbata, tare da fatan zai zame wa kasa alheri.
Shi kuwa shugaban Kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilai, Abubakar Bichi, ya yaba da tsarin, inda ya ce wannan sauyi da aka yi wajen tantance kasafin kudin da bin matakai daki-daki zai kawo wa kasa ci gaba wajen samu aikace-aikace.
Bichi ya ce akwai kyakkyawan fata na cewa za a ga sauyi sosai a rayuwar alu’mma tunda shugaban kasa ya riga ya sa wa kasafin kudin hannu.
Kafin wannan karin, ana bin Nijeriya bashi har na Naira Triliyan 87.38, wanda idan an hada da wannan, basussukan za su iya kai wa tirilyan 100 ko fiye da haka.
Sai dai Shugaba Tinubu ya yi wa majalisar bayanin cewa sauya shekar zuwa lamuni zai rage kudin biyan basussukan zuwa kashi 9 cikin 100 idan an kwatanta da tsarin hada-hadar kudi wanda ake karba a yanzu wanda ya kama kashi 3 cikin 100.
Hakan dai wani abu ne da masanan tattalin arziki ke cewa yawan bashi zai hana Nijeriya samun kudaden shiga da za su kawo wa talaka ci gaba mai ma’ana.