Majalisar Dattawa, ta umarci kwamitinta kan harkokin kuɗi da ya dakatar da ci gaba da tattaunawa kan ƙudirin haraji har sai an kammala wani babban taro da babban lauyan gwamnatin tarayya.
Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin ne, ya sanar da hakan a ranar Laraba, inda ya ce an kafa kwamiti na musamman da zai tunkari abubuwan da ake cece-kuce kan ƙudirin.
- Google, Microsoft, TikTok Sun Biya Gwamnatin Nijeriya Harajin N2.55trn A 2024 – NITDA
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar Sin
An shirya gudanar da muhimmiyar ganawar a ranar Alhamis 5 ga watan Disamba, don warware batutuwan da suka taso dangane da ƙudirin harajin.
Wannan ya biyo bayan zazzafar muhawara da ‘yan majalisar suka yi da nufin warware rashin jituwa kan batutuwan da suka shafi dokar.
Bugu da kari, shugabannin majalisar sun bayyana shirin yin wani taro na musamman da shugaban marasa rinjaye zai jagoranta, don cimma matsaya, tare da tabbatar da cewa ƙudirin ya yi dai-dai da muhimman abubuwan da suka shafi ƙasa baki ɗaya tare da magance matsalolin da masu ruwa da tsaki suka gabatar.
Kwamitin na musamman da aka ɗora wa alhakin warware matsalolin yana ƙarƙashin jagorancin, Sanata Abba Moro da Sanata Tahir Monguno da Adamu Aliero da Orji Uzor Kalu da Seriake Dickson da Titus Zam da Yahaya Abdullahi da Solomon Adeola, sai Sani Musa da Mukhail Abiru a matsayin mambobi.