Majalisar Dattawa, za ta gayyaci tsohon gwamnan babban bankin (CBN), Godwin Emefiele domin amsa wasu tambayoyi game da bashin naira tiriliyan 30 da gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta karba.
Majalisar dai za ta bukaci Emefiele ya yi mata bayani a kan wani bashin Naira tiriliyan 30 da ya bai wa gwamnatin tarayya a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
- Gwamnatin Tarayya Ta Gano Mutane 9, ‘Yan Canjin Kudi 6 Masu Tallafawa Ta’addanci A Nijeriya
- CIYARWA [Falalarta Da Muhimmancinta] Na 1
Shugaban kwamitin kula da huldar kudi tsakanin gwamnatin tarayya da CBN, Sanata Jibrin Isah ne, ya bayyana hakan jim kadan bayan zaman kwamitin da wakilan CBN a ranar Talata.
Isa, ya ce alamu na nuna cewa Emefiele ya zartar da wadansu hukunce-hukunce da a ka’ida bai kamata ya yi su kai tsaye ba.
Ya ce akwai bukatar ya tuntubi mambobin kwamitinsa, mataimakinsa da kuma masu ruwa da tsaki a lamarin.
Tuni dai majalisar ta kaddamar da wani kwarya-kwaryar kwamiti na musamman domin binciken yadda aka bayar da bashin da yadda aka kashe kudin da aka ranta.
Har wa yau, kwamitin da Sanata Jibrin Isah zai jagoranta zai binciki yadda aka bayar da bashin ‘Anchor Borrowers’ a zamanin gwamnatin Buhari.
Sanatan ya ce, “Mun duba kundin ‘ancho borrowers’ a gaban zauren majalisa, mun ga abubbuwa da yawa a cikinsa, mun dubi wadanda suka amfana da basukan.
“Wannan zai taimaka mana wajen gano gaskiyar abin da ya wakana a CBN a zamanin Emefiele.
“Babban abin da ya sa dole mu gayyaci tsohon gwamnan bankin shi ne wakilan CBN din da suka zo sun gaza amsa tambayoyin da mu ka yi musu, wanna shi ne zai tabbatar da cewa ba su da cikakken sanin abubuwan da suka wakana dangane da wadannan kudi da aka ranta wa gwamnatin tarayya.”
“Lallai idan shugabannin bankin na wannan lokacin suka gaza kawo mana bayanan da muke bukata, to ya zama wajibi mu gayyaci Emefielle ya gurfana a gabanmu domin fada mana yadda aka yi.”
Dangane da bashin manoma na ‘Anchor Borrowers’ kuwa, Isa cewa ya yi, “kawo yanzu an dawo da kaso 70, sauran kaso 30 din na wurin kananan manoma.
“Babban hatsarin da ke tattare da bai wa kananan manoma bashi, shi ne gaskiya ba su da wata dama ta kere sa’a, ko kuma kai wa ga tudun mun tsira, sakamakon yadda abubuwa suke.”
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa “kananan manoma ba su da kwarewar aikin noma na zamani, kuma ba su da kayan aiki, wannan matsala ce da idan aka yi wasa za ta hana mu samun abin da muke so.
Kwamitin majalisar ya bayyana cewa kudin da ke hannun kananan manoma yakai Naira Biliyan 358, amma inda ake sa ran samun sauki shi ne, an raba wannan rance ne ta hannun bankunan ‘yan kasuwa, don haka yanzu su za su san yadda za su yi su karbo kudin gwamnati.
CBN dai ya bai wa Gwamnatin Buhari rancen kudi kan tsaron da ake yi wa lakabi da “ways and means” a turance domin cike gibin kasafin kudi.
A yanzu haka dai Emefiele na tsare a hannun DSS, inda ya ke fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da cin amanar kasa da sauransu a kotu.