A yunkurin da ake na ganin cewa an inganta sashen Ilimi Nijeriya baki daya, majalisar dattawa ta amince da kudirin sauya Kwalejin Ilimi da ke Bichi a Jihar Kano zuwa Jami’ar ilimi ta Kimiya da fasaha.
Da yake zantawa da manema labarai kan kokarin da ya ke na ganin an samu nasarar aiwatar da aikin, Sanata mai wakiltar Kabo ta Arewa, Sanata Barau Jibril, ya tabbatar da amincewar da zauren majalisar ya yi na sauya Kwalejin Ilimin zuwa Jami’a.
- Mun Kashe Biliyan 7 Wajen Samar Da Ilimi Mai Nagarta —Gwamnatin Kano
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin Biliyan 10 Don Sayen Na’urar CCTV
Ya kara da cewa bayan nazarin kudirin da ‘yan majalisar suka yi na ganin an tabbatar da kudurin, mambobin majalisar sun gamsu da sauya Kwalejin zuwa Jami’a wanda a halin yanzu ake kan tabbatar da shi.
Sanata Barau, ya bayyana cewa wannan wata babbar dama ce ga al’umar kasar nan baki daya domin yin hakan zai kara inganta sashen Ilimin ta hanyar kara saukakawa mutane wurin samun wadataccen Ilimi cikin sauki.