Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
A wani zama ta gudanar ranar Jummu’a, zauren Majalisar dokokin jihar Borno ya jefa kuri’ar amincewa tare da jaddada gamsuwa da Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, tare da karyata labarin da wata kafar sadarwa dangane da cewa ‘wai’ ana zaman tsama tsakanin zauren majalisar da Gwamna.
Wannan sanarwar ya fito ne daga bakin Kakakin majalisar, Hon. AbdulKarim Lawan jim kadan bayan kammala taro na musamman da ta gudanar tare da cimma matsaya a zauren majalisar da ke birnin Maiduguri, wanda a lokacin zaman ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Zulum bisa namijin kokarin da ya nuna wajen shimfida nagartattun ayyukan ci gaban jihar baki daya.
Bugu da kari kuma, Kakakin ya kara da cewa, yan majalisar sun cika da mamaki a lokacin da su ka ga rahoton da wata kafar yada labarai ta fitar wanda ta alakanta zauren majalisar da daukar matakan yunkurin tsige Gwamna Zulum, mutumin da ya kasance abin kwatance ga kowa a fadin Nijeriya wajen gudanar da shugabanci nagari.
“Saboda haka, wannan zauren majalisa ya gudanar da zama tare da sake jaddada gamsuwarsa da tsarin shugabancin Farfesa Babagana Umara Zulum. Har wala yau, wannan zaure ba zai bata lokacin bayarwa wancan rahoton karya ba, face kawai mun ga hakan ya dace domin mu dakile tasirin wadanda su ka kirkireshi ga sauran jama’a tare da hana al’umma su yi wa lamarin gurguwar fahimta don su gano cewa baki dayan rahoton karya ce tsagwaronta, kana da la’akari da halin da jihar mu take ciki na rashin tsaro.”
“Sannan kowa shaida ne dangane da muhimman ayyukan ci gaban da gwamnatin Gwamna Zulum ta aiwatar wadanda su ka shafi kowane bangaren ci gaban tattalin arziki da walwalar jama’a. Haka kuma, bisa ga hakikanin gaskiya akwai kyakkyawar fahimta da aiki tare tsakanin bangaren zartaswa da na majalisar dokokin jihar Borno.”
“Har wala yau, ba mu taba fuskantar wata matsala tsakaninmu ba, ya dace ku barmu tare da kokari wajen taimaka wa Gwamnanmu mai himma da aikin da yake na sake gina yankuna tare da gamsuwar da jama’a ke nunawa a kansa. Kuma baki daya wannan zaure ya nisanta kanda daga wannan karyar da gidan jaridar ya wallafa tare da Allah wadarai dashi. Kuma muna kira ga jama’a su yi watsi da wannan rahoton kana muna kira ga hukumomin tsaro su ladabtar da wannan gidan jarida wanda ya kware wajen sharara karya.” Ta bakin Kakakin.