Shugaban majalisar dokokin Jihar Katsina, Hon. Nasiru Yahayya Daura ya ba da tabbacin majalisar za ta yi aiki kafada da kafada da bangaren zartaswar domin inganta tsaro da zaman lafiyar al’umma a fadin jihar.
Hon. Nasiru Daura ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a birnin Katsina.
Sabon shugaban majalisar dokokin ya bayyana cewa majalisar za ta yi aiki tare da bangaren zartaswar jihar domin shawo kan matsalar tsaron da ta dade tana cima wa al’umma tuwo a kwarya.
Ya ce za su hada hannu da karfe da bangaren zartarwa karkashin jagorancin gwamna Dikko Radda domin samar da kudurori da dokokin da za su kawo wa al’ummar jihar ci gaba, musamman wajen magance matsalar tsaron domin maido da zaman lafiya a fadin jihar.
“Abu na farko da wannan majalisar za ta yi shi ne, maida hankali domin tabbatar da kudurin gwamna Radda na maido da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar”, in ji shugaban majalisan.
Ya kuma bayyana cewa majalisar za ta tabbatar da inganta muhimman bangarorin zamantakewa domin bunkasa walwala da jin dadin al’ummar jihar, kamar a bangaren ilimi da noma da kiwon lafiya da samar da tsabtataccen ruwan sha.