Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Majalisar dokoki ta 10 a Nijeriya bisa amincewarta da ƙaddamar da dokar ta ɓaci (State of Emergency) a Jihar Ribas da kuma dakatar da gwamnan jihar da mataimakinsa da majalisar dokokin jihar daga aiki ta hanyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana mai cewa ‘yan majalisar sun zama kamar ƴan amshin Shata.
Kwankwaso, wanda ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kano sau biyu, ya ga baiken wannan mataki na majalisar, in da ya ce yayi kama da irin kuskuren da ‘yan majalisar tarayya suka yi a lokacin majalisa ta uku (Third Republic), wanda ya haifar da soke zaɓensu na ranar 12 ga Yuni, 1993. Ya bayyana cewa ƴan majalisar ya kamata ta juya wa wannan rashin adalci da shugaban ƙasa Tinubu ya aikata a Rivers, amma sun sai suka zaɓi goyon bayan wannan mataki wanda yake ba bisa ƙa’ida ba.
- Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume
- Jigon APC Ya Fara Yunkurin Sulhunta Kwankwaso, Ganduje Da Shekarau
Kwankwaso ya ci gaba da cewa wannan matakin da shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauka na dakatar da dukkan jami’an da suke zaɓaɓɓu a jihar Ribas ya saɓa wa kundin tsarin mulki, yana kuma kawo barazana ga tsarin dimokuraɗiyya. Ya bayyana damuwarsa game da yadda majalisar ta yi amfani da tsarin zabe na muryar wajen goyon baya (voice vote) wanda bai dace da ƙa’idojin zaɓe na ƙasa ba.
Kwankwaso ya ƙara da cewa wannan mataki na iya kawo matsala ga ci gaban dimokuraɗiyyar da aka samu cikin shekaru 26 na dawowarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp