An gabatar da wani kudirin doka da ke da nufin gyara sashe na 49 na kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, domin ware kujeru shida na musamman ga mata da nakasassu a majalisar wakilai.
Wannan shi ne karon farko da aka taba gabatar da irinsa a majalisar wakilai wanda har ya tsallake kaaratu na farko a ranar Laraba da ta gabata.
- An Gabatar Da Nagartattun Shirye-Shiryen CMG A Brazil
- Gwamnatin Tarayya Da EU Sun Kulla Yarjejeniyar Bunkasa Wutar Lantarki
Mai magana da yawun majalisar, Akintunde Rotimi (Ekiti, APC) ne ya gabatar da wannan kudiri na neman a kara yawan wakilai a majalisar daga 360 zuwa 366, na karin kujeru shida musamman na mata nakasassu.
A cewar kudurin dokar, za a raba kujerun na musamman a cikin shiyyoyin siyasa shida na Nijeriya, tare da tabbatar da wakilcin mutum daya daga kowace shiyya. Dole ne ‘yan takarar wadannan kujeru su cika dukkan ka’idar da ake bukata don zama mamba a majalisar wakilan Nijeriya.
Za a gudanar da zaben wadannan mukamai ne ta hanyar kwalejin zabe da ta kunshi mambobi daga kungiyoyin nakasassu na kasa, tare da gudunmawa daga matakan kasa da na yanki a cikin tsarin zabe mai yawa.
Da zarar an zabe su, wakilan za su yi wa’adi daya da sauran ‘yan majalisar kuma za su sami alfanu daidai wa daidai kamar yadda kudirin ya bayyana.
Rotimi ya bayyana cewa kudirin dokar na da nufin bunkasa wakilcin mata da nakasassu, wadanda galibi ke fuskantar cikas ga harkokin siyasa.
“Kirkiro wadannan kujeru na musamman zai tabbatar da cewa ana jin muryoyin kungiyoyin da ba su da wakilci a matakin kasa, tare da samar da daidaito da kuma tsarin majalisar dokokin Nijeriya,” in ji shi.
Idan dai za a iya tunawa, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, a ranar Litinin ya ba da shawarar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar na tanadar kujerun majalisar dokoki ga mata da kuma tabbatar da shigar da su cikin mukamai a majalisar zartarwa.
A wani labarin kuma, Cibiyar Nazarin Dokokin Majalisa da Dimokuradiyya ta Kasa (NILDS), ta bayyana wakilcin mata a majalisar dokokin Nijeriya, wanda a halin yanzu bai kai kashi 10% a matsayin abin kunya ba.
Wakiliyar NILDS, Titilayo Daniel ta bayyana hakan ne a jiya a yayin wani taro da aka gudanar a garin Sagamu na Jihar Ogun, inda aka mayar da hankali kan wayar da kan ‘yan majalisar mata mai taken, “Karfafa wakilcin mata a siyasance.”
Da take jawabi ga ‘yan siyasa mata sama da 100, Daniel ta bayyana muhimmancin daidaita jinsi a majalisar dokoki ta kasa. Ta ce, “Mata ba su kai kashi 10 cikin 100 na ‘yan majalisar dokoki ta kasa ba, ma’ana cewa sama da rabin al’ummarmu ba sa cikin masu yanke hukunci. Wannan kididdigar abin kunya ce ga Nijeriya idan aka kwatanta da sauran kasashen Afirka kamar Rwanda, wacce ke da kashi 61.3% na wakilai.”
Daniel ta kara da cewa matan Nijeriya na ci gaba da fuskantar cikas da dama ga shiga harkokin siyasa, tana mai nuni da cewa tsarin majalisar dokokin na nuna san kai.