Majalisar Wakilai ta bayyana buƙatar ɗaukar ma’aikata masu yawa a jami’o’in Nijeriya domin magance matsalar barin aiki da malamai da ma’aikatan jami’o’i ke yi, wadda ta fi shafar rashin kyakkyawan albashi. Kakakin kwamitin ilimi, Hon. Fulata, ya ce gwamnati na bukatar duba albashi da karin hakkoki ga ma’aikatan jami’o’i cikin gaggawa domin dakile wannan matsala.
Hon. Fulata ya yi kira ga Shugaban Kasa da ya bai wa jami’o’i damar gudanar da daukar ma’aikata da yawa domin cike gibin ma’aikata. Ya kara da cewa wasu sun bar aiki yayin da wadanda suka rage suna wahalar yin ayyukansu saboda yawan aiki. Haka zalika, ya bukaci a karawa ma’aikatan jami’o’i albashi da hakkoki don rage barin aiki saboda rashin jin dadin albashi.
- Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
- Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Koka Kan Barazanar Tsaro, Ta Nemi Gwamna Ya Ɗauki Matakin Gaggawa
Ya kuma gargadi gwamnati da ta daina tsoma baki ba bisa ka’ida ba a harkokin gudanarwar kwamitocin jami’o’i, inda ya ce wannan na hana jami’o’i gudanar da aikinsu yadda ya kamata kuma yana raunana ‘yancin gudanarwa. Kwamitocin gudanarwa na da ikon daukar ma’aikata ko sallamar ma’aikata, amma hakan bai fi ye samuwa ba saboda tsoma bakin wasu hukumomi.
Hon. Fulata ya kuma roki Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta dakatar da shirin yajin aiki, yana mai cewa yawan yajin aiki na kara matsaloli da tabarbarewar tsarin karatu a jami’o’i. Ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa kwanan nan ya ziyarci jami’o’i a fadin kasar don ganin matsalolin da suke fuskanta, wanda ya bai wa mambobin kwamitin damar fahimtar matsalolin da ake ciki.














