Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta cafke wani yaro dan shekara 15 a duniya, Adamu Ibrahim, bisa zarginsa da sara hannun hagun wani manomi biyo bayan rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu.
Binciken ‘yansanda ya nuna musu cewa a ranar 24 ga watan Agustan 2023, wanda ake zargi (Adamu Ibrahim) dauke da sanda da adda ya shiga cikin gonan wanda lamarin ya shafa tare da lalata masa amfanin gonar da har yanzu ba a kiyasce adadinsu ba.
- EFCC Da CCB Sun Gayyaci Muhyi Magaji Rimin Gado
- Mutane 12 Sun Mutu, 80 Sun Jikkata A Bikin Bude Wasanni A Madagascar
A wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar Bauchi, Ahmad Muhammad Wakil ya fitar a ranar Asabar, ya ce, bayan barkewar rashin jituwa a tsakaninsu, wanda ake zargin ya sara hannun manomin da adda biyo bayan neman da ya yi masa da ya fice masa daga cikin gona.
Wakil ya ce, “Shi wanda ake zargin ya zaro adda tare da daba wa hannun daman manomin.”
Kazalika, binciken ‘yansanda ya kara gano musu cewa shi Adamun ya saba shiga cikin gonar manomin da shanunsa domin kiwo.
Ya ce, an fara kai ruwa-rana tsakaninsu ne biyo bayan jerin korafe-korafen da manomin ya kai wa mahaifin Adamu da ke cewa yana shiga gonarsa domin lalata masa amfanin gona.
“Bayan samun faruwar lamarin, kwamandan ‘yanki ya tashi tsaye domin shiga cikin lamarin domin kauce wa matakin da zai kai a je matakin fada tsakanin manomi da makiyayi wanda hakan ya sanya suka kamo wanda ake zargi,” in ji jami’in watsa labaran.
An garzaya da manomin zuwa asibitin koyarwa na ATBUTH kuma a halin yanzu yana kan murmurewa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi CP Auwal Musa Mohammed, ya gargadi manoma da suke kauce wa shiga cikin gonakan mutane a fadin jihar domin kauce wa samun rashin fahimta.
Kwamishinan ya umarci a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike.