Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
A daren Alhamis zuwa wayewar gari ne al’ummar Sabon Titi da ke Tungan Ɗanboyi cikin garin Minna suka wayi gari da abin al’ajabi na yadda malamin allo ya ɗaure almajiri yayi mai dukar da sai da aka kwantar da shi a asibiti.
Ganau sun shaida wa jaridar LEADERSHIP A Yau cewa, malamin ya ɗaure almajirin ne hannu da ƙafa da roba inda yayi ta dukanshi har sai da ya lalata mishi dukkan jiki da bulala, wanda sanadiyar ɗaurin ma ya sanya yaron bai iya amfani da hannunshi.
Da yake amsa tambayoyin wakilinmu akan gadon babban asibitin Minna, almajirin mai suna Aminu Mu’azu Bebeji, ya ce, malamin ne ya ɗauko su daga garinsu na Bebeji ta Jihar Kano, don yin karatun allo, sai ya kasance shi bai samu zuwa makaranta a wani dare don yin karatu ba saboda gidan da yake masu aiki ya iske aikin yayi yawa, bayan ya dawo ya kwanta cikin dare sai malamin nasu mai suna Ayuba Muhammed ya ɗaure shi da roba hannu da ƙafa ya yi ta dukansa. Bayan ya ji masa raunuka a jiki kuma ya barshi a ɗaure ɗin har sai da ya galabaita sannan ya samu taimako daga wasu bayin Allah. Wanda bayan an kwance shi ya zama bai iya amfanar kansa saboda yunwa da galabaitar dukan da ya sha, kuma hannunsa ma bai iya ko riƙe kofi da su.
Amma maganar lalacewar hannun almajirin, ya ce, shi ne ya haddasa hakan don shi ne ya yi ta ƙoƙarin ganin sai ya kwance kanshi daga ɗaurin wanda ya janyo mai jin ciwo haka. A cewar shi lallai ya daɗe yana koyarwa amma hakan bai taɓa faruwa da shi ba.
Yayin da LEADERSHIP A Yau take tattaunawa da babbar darakta mai kula da haƙƙin yara ta Jihar Neja, Barista Maryam Haruna Kolo, ta ce, lallai da yammancin Juma’a ne aka kawo mata rahoton wani malamin allo ya yiwa almajirinsa dukan da ya zama yaron bai iya tashi, jin hakan ta tura jami’anta wanda bisa tilas ta miƙa malamin a hannun jami’an tsaro don yin kyakkyawan bincike a kansa. Ta ce; “domin a yadda na ga yaron nan, hankali ba zai amince cikin hayyacinsa yayi wannan ɗanyen hukuncin ba. Yaron yanzu haka ya na ƙarƙashin kulawarmu yana kwance a babban asibitin gwamnati da ke Minna, yana samun kulawar likitoci. Yayin da shi kuma malamin mai suna Ayuba Muhammed a ke ci gaba da bincikensa, wanda da zaran jami’an tsaro sun kammala aikinsu cikin makon nan za mu miƙa shi gaban alƙali. Makarantar kuwa dole a rufe ta, su kuma sauran almajirai gwamnati za ta mayar da su wajen iyayensu.” Inji ta
Binciken da wakilinmu yayi akan lamarin malam Ayuba Muhammed, an tabbatar da cewa ba wannan bane karonsa na farko da yake irin wannan hukuncin ga almajiransa.