Connect with us

ADABI

Mallam Bahaushe Ga Naka (4)

Published

on

Matakin karshe shi ne fitar imani. Wadannan zantuttuka duk Atika da Turai ke yin su a cikin dakinta. Tare da yin nuni da cewa matukar Baballe bai dawo ba, to sai matakin gurbatar zuciyarsa ya kai shi ga wannan fagen. Har ma ta ke shaida mata cewa ‘ya’yanta uku duka ta san cewa su na yin karuwanci, duk babu ce ta haddasa masu haka. Turai ta dube ta da mamaki cike da fuskarta. ‘Ah, to ina marabar dambe da fada, ina marabar karuwanci da abin da su Luba ke yi, tunda zuwa ake yi a dauke su a tafi a yi lalata da su a dauki abin Duniya a basu, a dawo da su gida. Kin ga ko ba a yi karuwanci ba ai an zama mage-da-wuri’.
Ta kara ba Turai haske na illolin da talauci ke jawowa har da roko da garamci da damfara da wala-wala. In mutum na da wadata to wallahi ko an ce ya zo ya yi sana’ar roko za ya ce ba za ya yi ba. Turai ta tambayeta ‘to kwartanci fa ?, Shi ma talauci ke kawo shi?’. Atika ta ce kwartanci ga da namiji ciwo ne na musamman a jikin mutum, ba talauci ke kawo shi ba, amma ga diya mace talauci ko rashi ke haddasa shi.
Daga karshe Atika ta ce ma Turai duk da haka sun yi murna da zaman Baballe a can Ilarsu tunda ya na cikin koshin lafiya kuma ba a hannun hukuma ya ke ba, ba kuma a bias gadon asibiti ya ke ba. Har ta ce mata ‘da Allah Ya hukunta a yanzu ya na can Ilarsu ya na jiyya, to da jiyyarsa ba za ta yi bambamci da jiyyar akuya ba, saboda idan akuya na jiyya ba ka ganin kowa kusa da ita. Turai ta ce mata ‘ki na nufin akuya ba ta da amfani?’. Atika ta ce ‘To wa ke tsoron akuya, tunda ba ta cizo, ba ta tunkuyi’. Ita ko jiyya ana yi ma wanda ake tsoro ko wanda ake kwadayin abin hannunsa. To shi Baballe a can Ilarsu, ba mai tsoronsa ba mai kwadayin abin hannunsa tunda bay a da shi. Ita kuma akuya minene amfaninta in bay a ga haihuwa ga mai ita? Sai ko a tatsi nononta a yi dakashi. Turai ta ce ‘hakane kuma wallahi’. ‘Amma minene dakashi?’, in ji Turai. Sai Atika ta ce mata idan kin koma gida in hutun ki ya kare ki tambayi kakarki ta fadi maki. Gaba dayansu su ka fashe da dariya. Turai ta ce mata ‘to ni dai na biyo ki bashi sai kin fadi mani ma’anar wannan kalma tunda ban sani ba ko kafin in koma gida Allah Ya dauki raina.
Babi Na Uku: Tsugunne Ba ta Kare ba
Safiyar Litinin, wata tsohuwar mota mai kamar a kai ta bisa juji a yada wadda kuma aka daina yayi ta sauka tashar motar Katine. Fasinjoji kusan arbaminya da su ka fi karfin motar su ka yo waje. Daga cikinsu sai ga wani komadadde mai kusan shekaru saba’in ya fito ya na dangyashi kamar gurgun kwaddo, cakal-cakal. Da ganinsa ka san ya gaji. Ga shi busashshe, ya na dauke da ‘yan kunshin kaya kamar kwarton da aka koro. Kai, da ganinsa ka ga sakarai shashasha, wanda Duniya ta dade da yi ma gwalo. Ya na sanye da wani dan guntun rawani kamar ragamar rakumi. Duk inda ya gitta ya na kauri kamar ana gasa tsuntsu. Mutane na ta kallon sa. Amma da ya isa gidan da ya bar matarsa Atika da ‘ya’yansa na haya sai aka ce sun tashi tuni, kusan shekaru uku da su ka gabata. Aka hada shi da wani yaro ya kai shi inda su ka tare, Tudun Galadima. Ya tarar babban dan sa Bala wanda talauci ya hana ya je makaranta ya yi kokari ya fara sana’ar Babura, shi ya kokarta ya gina masu gidan. Har ma mutanen unguwar na yi mata ba’a sun a cewa da ba don Bala ba da ba a kiranta ta amsa saboda babu.
Kwanaki kadan masu zuwa. Hidimar gidan su Atika ta dauki sabon salo. Ga ta dai cikin gajiya da rashi, babu abubuwan more rayuwa, abin ci ma wahala ya ke yi masu. Ga ‘yammata da jawarawa a gabanta, kuma ba kimtsatstsu ba. Nauyi dai ta ko’ina ya haye mata, to sai kuma ga Baballe, shi ma ya dawo da nasa matsalolin. Daga dan dakin da Atika ke kwana ta na kuma ajiye tarkacenta, dan karami kamar dakin tantabaru, dole ta tashi ta bar masa ya shinfida ‘yan tsunmokaransa ya na kwana ciki. Allah Sarki, talaka bawan Allah. Wannan shi ne Hausawa ke ce ma an fado daga iccen dabino an zarce cikin rijiya. Shikenan, rayuwa ta ci gaba da tafiya a haka. Kullum ba dadi. Idan ya kira yaran say a aike su sai sun ga dama su je. Don dan karamin ma ya na iya zagin sa. Saboda mi? Saboda bas u tashi su ka gan shi a gaban su ba. Uwarsu kadai su ka sani a matsayin main emo masu abin ci, ita ce mai dunka masu rigunan makaranta da na sallah, ita ce duk wahaar su. Don haka ba ya da ikon kwaba masu, ko da kuwa ya ga sun yi wani abu ba daidai ba. Cikin su ba mai ganin daraja ko girman sa a matsayin uba. Ga kuma Turai a ko da yaushe ta na ta zarya a gidan kamar kiyashi. Duk ba su san digimirshin da ake ciki ba. Baballe, kullum sai ya aika Turai ta saya masa goro ko kunun zaki da ake yi a makwabta bai san sunan sa na can Amerika ba ta kai ana nazarin sa.

Advertisement

labarai