Akalla mutane shida ne aka ce sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a karamar hukumar Kafin-Hausa ta jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar, Muhammad Saminu ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan wasu da abin ya shafa.
A cewarsa, mutane 6 ne suka mutu, yayin da wasu 60 suka samu raunuka tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira sakamakon mamakon ruwan sama da iska da aka yi a yankin.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa, guguwar ruwan sama da ta afku a daren Talata, ta sa daruruwan iyalai sun rasa matsugunan su, lamarin ya tilasta musu samun mafaka a gidajen jama’a da gidajen ‘yan uwa.