• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Man Girki Mara Asali: Kamfanin Power Oil Ya Kulla Alaka Da Ali Nuhu Kan Wayar Da Kai

by yahuzajere
2 years ago
Girki

Kamfanin Man Girki na Power Oil ya sanar da kara fadada gangaminsa na inganta kiwon lafiya a Arewacin Nijeriya. Kamfanin wanda ya fara kaddamar da man girki mai kyau a Nijeriya kuma kwanan nan ya yi hadin gwiwa da Ali Nuhu Mohammed (dan wasan kwaikwayo na Nijeriya kuma darakta wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood) ya bayyana cewa za su shiga wani gangami a kan wayar da kan jama’a game da salon rayuwa mai inganci.

Gangamin zai fadakar da mutane kan yadda ake amfani da man girki sahihi tare da kauce wa amfani da irin man da ba a san asalinsa ba ko sunan kamfanin da ya sarrafa ba a Nijeriya.

  • Gwamnan Gombe Ya Bada Umurnin Rufe Dukkanin Gidajen ‘Gala’ Da Ke Jihar Nan Take 

Tsawon shekaru, man girki marasa asali sun samu gindin zama a cikin rumfunan kasuwar Nijeriya tare da shiga gidaje daban-daban ta hanyoyin da ba za su kididdigu ba. Akwai irin wannan man girki a cikin kwantenoni, sannan abin takaici yana haifar da rashin lafiya saboda rashin inganci da tsaftar da ta kamata a kiyaye yayin sarrafawa.

Wani abin la’akari shi ne yanayin tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa a cikin kasa babu shakka sun sa magidanta cikin tagumi, don haka ake da bukatar kowa ya rika lura da yadda yake kashe kudin aljihunsa. Shi ya sa talakan Nijeriya a koyaushe ya gwammace ya rika make kudinsa tare da sayen gurbatattun abubuwa maimakon wadanda za su kiyaye koshin lafiya.

 

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

Daya daga cikin irin wadannan abubuwa shi ne man girki; wanda ake amfani da su a kai a kai a cikin kicin. Domin samun biyan bukata, talakawan Nijeriya sun zabi man girki mara sinadari wanda ke da araha kuma yana kara hadari ga lafiyar zuciya.

 

Kwararrun likitoci da hukumomin da abin ya shafa kamar Gidauniyar Kula da Cututtukan Zuciya ta Nijeriya (NHF) da sauran su sun yi gargadi game da shan wadannan kayayyakin da ba su da asali wadanda ka iya dauke da sinadarin kara kitse mara amfani (cholesterol) mai yawa. Kasuwar irin wannan gurbataccen mai na ci gaba da hauhawa yayin da kwayar kitsen cholesterol da cututtukan zuciya ke haddasuwa a cikin rayuwar masu amfani da su. A cewar kwararrun likitocin, cholesterol na da matukar hadari ga cututtukan zuciya a tsakanin mutane masu shekaru daban-daban.

Sakamakon kudirin fadakar da ‘Yan Nijeriya hanyoyin kiwon lafiya tare da Jarumi Ali Nuhu, Man Girki na Power Oil wanda ba ya dauke da ‘cholesterol’ ko kadan da sauran sinadarai na gina jiki yana fatan ya leka lunguna da sako na arewacin Nijeriya domin wayar da kan a kan amfani da man girki mara suna da asali, kana da ilmantar da ‘Yan Nijeriya a kan yadda za su rika gudanar da rayuwa cikin koshin lafiya.

Ali Nuhu Mohammed wanda wasu suke masa laƙabi da “Sarki Ali” ana xaukarsa a matsayin wani jigo musamman a tsakanin matasan Arewa; ya samu lambobin yabo da karramawa daga sassa daban-daban, wanda hakan ne ya ba shi damar zama mafi dacewa wajen jagorantar gangamin. Zai yi amfani da shuhurarsa tare da tasirin da yake da shi wajen jagorantar da gangamin hana amfani da man girki maraasali.

Wakazalika, Man Girki na Power Oil yana shirya motsa jiki na musamman wanda kowa da kowa zai iya halarta. Tun daga 2015 aka kaddamar da shirin inda likitoci daga sassan kiwon lafiya da dama ke halarta domin wayar da kan jama’a a kan rayuwa mai inganci.

 

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025
Labaran Kasuwanci

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya
Labaran Kasuwanci

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

June 21, 2025
Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman
Labaran Kasuwanci

Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman

January 11, 2025
Next Post
Yawan Sinawa Masu Amfani Da Intanet Ya Kai Fiye Da Biliyan 1

Yawan Sinawa Masu Amfani Da Intanet Ya Kai Fiye Da Biliyan 1

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025
Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

October 21, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

October 21, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi

October 21, 2025
Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.