Kungiyoyin Manchester United da Arsenal sun ja layi akan dan wasa Leon Goretzka na Schalke. Dan wasa Leon wanda yake bugawa kungiyar wasan kwallon kafa ta Jamus, kwantiraginsa da zata kare nan ba da jimawa ba; ya samu tayi daga Bayern Munich da Barcelona.
Banda wannan, kungiyar Manchester United ta kwallafa rai kan dan was an baya na Celtic, Kieran Tierney, kamar yadda kafar ‘Daily Record’ ta wallafa. Sannan kuma ga zaren da suka sa da kungiyar Arsenal akan Goretzka.