Abba Ibrahim Wada" />

Manchester United Za Ta Sayar Da Pogba A Karshen Kakar Wasa

Pogba

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta shirya sayar da dan wasa Paul Pogba a karshen kakar wasa idan har aka samu kungiyar da za ta iya biyan abinda kungiyar ta saka akansa.

A ranar Juma’a ne mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa, dan wasa Paul Pogba ya kama da wuta kuma yana daya daga cikin wadanda za su kai kungiyar inda suke fata a wannan kakar.

Solkjaer ya tabbatar da hakan ne a daren Juma’a bayan da dan wasan ya zama dan wasan da ya fi nuna bajinta a fafatawar da kungiyar ta samu nasara da ci 2-1 akan kungiyar Aston Billa kuma nasarar da ta sa yanzu kungiyar ta ke maki daya da Liverpool wadda za ta buga wasa da Southamton idan an jima.

A kwanakin baya ne wakilin dan wasa Pogba kuma mai kula da harkokin wasanninsa, Mino Rioala, ya bayyana cewa, Pogba ba ya jin dadin wasa a Manchester United ya kamata ya sauya kungiya a watan Janairu lamarin da ya haifar da cece-kuce kuma wasu suke ganin da amincewar Pogba wakilin nasa yayi wannan maganar.

A watan Yunin shekara ta 2022 kwantiragin dan wasan tawagar Faransa zai kare, zai kuma iya barin Old Trafford a watan Janairun shekara ta 2022 a matakin wanda bai da yarjejeniya kuma Pogba mai shekara 27, ya buga wasanni goma a gasar Premier League har da shida da aka fara bugawa da shi a fili a kakar bana.

Amma Pogba, wanda ya sake koma wa Manchester United daga Juventus a shekarar 2016, bai boye aniyarsa ta buga wasa a Real Madrid nan gaba ba kuma a watan Nuwamban da ya gabata kociyan tawagar Faransa, Didier Deschamps, ya sanar cewa, Pogba ba zai taba samun farin ciki a United ba a lokacin da kungiyar ba ta samun nasara a wasanni. Sai dai yanzu abubuwa sun fara canja a nasarar kungiyar.

Exit mobile version