A yayin da ake fara noman farin wake da auduga a wasu sassan kasar nan, wasu manoma sun rungumi sabon tsarin yin amfani da irin noma da aka samar ta hanyar fasaha, musaman domin su kara bunkasa noman amfanin gonar guda biyu da kuma kara samar wa kansu da kudi da kuma magance musu yin asara.
Samfirin irin na farin wake shi ne, SAMPEA 20-T, wanda akasarin manoma da dama suka runguma don yin noman nasa.
Irin wanda aka samar da shi aka kuma fitar da shi, wasu kwararru a cibiyar bincike iri ta jami’ar Ahmadu Bello da ke zariya (IAR), ta samar karkashin kulawar Gidauniyar binciken amfanin gona ta fasaha, da ke Afirka(AATF).
Samfarin na SAMPEA 20-Tna na irin farin wake na yakar ko wace irin cuta da ka iya yi wa waken illa.
Ko a bara, saboda daukewar ruwan sama da wure tare da kuma aukuwar dumamar yanayi, ya jawo wa wasu manoma rashin samun amfani mai yawa.
Wasu manoma a wasu sasan kasar nan sun amfani da wannan sabon irin a gonakinsu, kuma suka samu amfanin mai yawa, wasu manoman a kadada daya suka samu fiye da kusan tan 3 na waken da suka shuka.
A cewar manoman da suka yi amfani da irin a bara sun sanar da cewa, irin ya rage musu yin asara da rage kashe kudin sayen maganin feshi. Jimlar manoman wake a kasar nan sun kai dubu 820 da suke yin nomansa a jihohi 15.
Wani mai bincike a IAR Dakta Mohammed Lawan ya ce kamata ta yi manomanm na farin wake a kasar nan su rungumi wannan irin, musamman ganin cewa, irin na da saurin yi in an shuka shi.
Dakta Mohammed ya ci gaba da cewa, irin na kai wa daga kwanuka 75 zuwa kwanuka 80 kafin ya kammala yi, wanda ya yi nuni da cewa, manoman da ke yin nomaansa a jihar Neja da Filato, na kammala yi daga kwana 65 zuwa kwana 75.
Ya shawarci manoman na Farin Wake da su tabbatar da sun bi ka’idojin da aka shimfida yayin shukarsa, musamman ta hanyar bayar da tazara daga santi mita 75 zuwa santi mita 20 wajen shuka.
Shi ma shugaban kungiyar manoma ta kasa Kabir Ibrahim ya bayyana cewa, fasar zamani da aka yi amfani da irin na PBR kuma ya samu amfani mai yawa, inda ya bayyana cewa, yin amfani da shi, zai taimaka wajen yakar talauci, samun raguwar yin asara ga manoman wake da kuma kara samun zuba jari a fanin aikin noma a kasar.
Kabir ya ci gaba da cewa, zan iya tabbatar da ingancin wannan irin na Farin Wake domin na yi amfani da shi naga ingancin sa.
Sai dai, akwai wani tsoron da ake ji wajen yin amfani da Farin Waken da aka samar ta hanyar fasa, inda wasu ke ganin zai iya shafar kiwon lafiyar ‘yan Adam.
Amma wasu masana a fannin noman fasaha sun bayyana cewa, babu wata illa da za ta samu mutanen da suka ci wannan farin waken, inda suka kara da cewa, domin kafin a fitar da shi sai da hukomar kula da aikin noma ta BAN suka amince da shi.
Wani ma’aikacin noman rani da ke yin aiki a Yawuri cikin jihar Kebbi Alhassan Yusuf Libata ya bayyana cewa, manoma da dama sun nuna sha’awar su ta yin amfani da wannan irin na farin Waken.
Sai dai, Alhassan ya gargadi manoman na wake da su guje wa shuka irinsa da wuri, domin irin na fara futar da fure ne a cikin kwanuka 40 bayan an shuka shi.
A bangaren noman auduga kuwa,an samar da samfarin da ake kira Bollgard II ko kuma a kira shi da (Mahyco C 567 BG2 and 571 BG2).
Wannan irin dai, tuni wasu manoman na Audugar a johar Filato, da Adamawa da Kano da Katsina da Gombe da kuma a wasu sassan kasar nan.
Wannan irin na Bollgard na yakar ko wacce irin cuta da ke yi wa amfanin illa.
Wani malamin noman rani a jihar Kano Alhaji Lawal Abdullahi ya bayyana cewa, manoman na Audugar da daman a son yin amfani da wannna irin a noman bana, musaman idan sun samu shiga cikin shirin aikin noma na gwamnatin tarayya wato Anchor Borrowers.
Abdullahi ya ci gaba da cewa, ingancin da irin yake da shi ne ya sa manoman na augugar suke ci gaba da nuna bukatarsa.
Wasu masana a fannin aikin noma a kasar nan, sun yi nuni da cewa, yin amfani da wannan irin zai iya taimak wa wajen farfado da masakun kasar nan da suka riga suka durkushe.
In za a iya tuna wa, duk da naira biliyan 100 da gwamnatin ta bayar ta hanyar bankin masana’antu don a farfado da masakun, har yanzu babu wani abin da aka yi.
Noman auduga a kasar nan, na ci gaba da raguwa, har sai da aka samar da samfarin irin na auduga da ake kira Bt a 2019, wanda a yanzu yak e ci gaba da janyo hankalin manoman na Auduga ganin yadda suke yin amfani da shi.
Manoman Audugar da dama a Jihar Adamawa a yanzu na yin amfanai da shi inda hakan ya kara masu samun riba.
Masana a fannin noman auduga sun bayyana cewa, yin amfani da irin na maganace kalubalen dumamar yanayi da kuma yakar duk wata cuta da ke yiwa amfanin gona illa.
Darakta Janar nariba hukumar habaka noman fasa da bunkasa aikin noma ta kasa NABDA Farfesa Abdullahi Mustapha ya bayyana cewa, canjin da aka samu na dumamar yanayi ya bayar da dama ga manoman Audugar a kasar nan rungumar yin mafnai da irin, musamman ganin cewa, irin na rage wa manoman yin asara bayan sun yi girbi.
Ita ma wata jami’a a hukumar NBMA Hauwa Tahir Ahmed ta sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta samar da matakai da dama domin a amfana da fasar zamani ta yin noma.
Shi ma Darakta a Cibiyar gudanar da bincike a fannin aikin noma ta kasa da ke a jihar Neja Dakta Dakta Muhammed Ishak ya bayyana cewa, yin amfani da irin zai taimaka matuka wajen kara habaka noman Auduga a kasar nan.