Wata gidauniyar shirin ‘ya’yan Itatuwa da ke gudanar da aikinta a Nijeriya, wato (HortiNigeria), ta wanzar da wani shiri nata na yakar cutar da ke lalata Tumatirin da manoma suka shuka, wanda a turance ake kira da suna ‘Tuta Absoluta’.
Gidauniyar ta wanzar da shirin ne a Jihohin Kano, Kaduna da kuma a sauran wasu jihohi uku, a karkashin shirin aikin noma na Kasar Jamus.
- Yau Kotun Tarayya Za Ta Yanke Hukuncin Masarautar Kano
- Daga Kai Kuɗin Fansa ‘Yan Bindiga Sun Kashe Shi A Dajin Kachiya
Har ila yau, ta yi hakan ne; domin sama wa manoma kayan aikin da za su yaki wannan cuta da ta jima shekara da shekaru tana addabar Tumatirin da manoma suka shuka.
Kazalika, Gidauniyar ta wanzar da wannan aikin ne ta hanyar yin hadaka da wasu masu ruwa da tsaki a wadannan jihohi da abin ya shafa.
A karkashin hadakar, manoma Tumatirin kimanin 60,000 ne za su amfana da sabbin kayan aikin na zamani, domin yakar cutar ta mai suna ‘Tuta absoluta’ a Jihohin Kano da Kaduna da kuma sauran wasu jihohi uku.
Jagoran aikin tare da fadakarwa na Gidauniyar, Malam Abdullahi Umar ya sanar da hakan ne a yayin taron wayar da kan manoman Tumatirin, wanda Gidanuniyar ta gudanar a gonakin wasu daga cikin manoman da cutar ta bulla a bangaren nasu.
Haka zalika, Gidauniyar ta yi taron ne a karkashin wani aikinta na kare kwarin da ke yi wa Tumatir din da aka shuka illa, wato (IPM).
A cewar Abdullahi, “Manoma Tumatirin sama da 60,000 da ke Jihohin Kano da Kaduna sauran wasu jihohi ne muke sa ran za su amfana da kayan aikin na zamani”.
Ya ci gaba da cewa, a karkashin aikin za a horar da manoma a yankuna daban-daban da ke fadin jihar.
“Mun jima muna karfafa wa manoman Tumatir gwiwa, musamman a kan cewa kada su sake su gaza wajen ci gaba da yin wannan noma na Tumatir, sakamakon bullar wannan cuta; domin kuwa muna da yakinin cewa; akwai yadda za a yi a iya magance cutar ba da jimawa ba, da yardar Allah”.
Kazalika, ya kuma sake bayyana cewa; muna nan muna ci gaba da kokarin sama wa wadannan manoman na Tumatir kasuwa, yadda za su rika sayar da shi cikin sauki tare kuma da samun kudaden shiga a cikin aljihunansu.
Shi ma a nasa bangaren, wani kwararre a cikin aikin; Mista Sabastine Agada Obaje ya yi nuni da cewa, yin gwajin na da matukar mahimmanci, domin kuwa ta hanyar yin gwajin ne za a iya taimaka wa manoman yin amfani da dabarun fasahar zamani wajen yin wannan noma na Tumatir.
Guda daga cikin manoman Tumatirin, Malam Uba Bello a nasa jawabin a wajen gwajin ya bayyana cewa, taron ya kara wa manoman Tumatirin kwarin gwaiwa, kan yadda za su tunkari kalubalen bullar cutar a gonakinsu.
A cewar tasa, sabuwar fasahar zamanin; tabbas za ta taimaka wa manoman Tumatir, kan yadda za su kara habaka sana’arsu ta wannan noma na Tumatir.
Ya kara da cewa, hakan zai kuma bai wa sauran manoman; musamman wadanda cutar ta sa suka dakatar da yin noman Timatirin samun damar dawowa cikin sana’ar gadan-gadan.