ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Ƙalubale Takwas Da Ke Shafar Farashin Tumatir

by Abubakar Abba
5 months ago
Tumatir

A kusan ƙarni biyu da suka gabata, wasu ƙwararru da masana a fannin aikin noman ƙasar nan, sun danganta ɗimbin dalilan da suka sanya ake yawan samun hauhawar farashin tumatir a kasuwancinsa da ake yi a wannan ƙasa, wanda hakan ke shafar manoman da ke noma shi da kuma masu sayen sa, domin amfanin yau da kullum.

Kashi 65 na tumatirin da ake kai wa ƙasashen Afirka ta Yamma, daga Nijeriya ake fitar da shi duba da cewa; Nijeriya ce  ƙasa ta biyu a Afirka da ke noman sa, wadda kuma ta kasance ta 14 a duniya, wajen noman shi.

Sai dai, Babban Shugaban Cibiyar Bincike ta NIHORT, dakta  Ephraim Nwanguma ya bayyana cewa; duk shekara, Nijeriya na shigo da kimanin tan  150,000 na tumatir daga ƙasashen ƙetare, wanda kuɗinsa ya kai kimanin dala miliyan 170 duk da cewa; ƙasar na iya yin nomansa da yawa.

ADVERTISEMENT
  • Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025
  • Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025

Ya ƙara da cewa, Nijeriya ce ta uku a Afirka wajen shigo da tumatirin gwangwani Afirka, inda ta kai mataki na 13 a duniya wajen shigo da shi cikin ƙasar.

 Kazalika, sashen kula da samar da abinci na Majalisar ɗinkin ɗuniya (FAO), ya danganta wadannsn ƙalubale a kan asarar da manomansa suke yi, mussaman a farkon girbe shi, wacce take kai wa ta kusan kashi 50, inda suke samun kashi 20 kacal, na wadanda suka noma.

LABARAI MASU NASABA

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

A bisa ƙiyasin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya yi, ya ce; tumatirin da ake nomawa a   shekara a Nijeriya, ya kai kimanin tan miliyan 1.701, wanda kuma ake amfani da shi a shekara ya kai aƙalla tan 2.93, inda wannan adadin ya nuna cewa; a shekara, ana samun ƙarancinsa da ya kai na kimanin tan miiyan miliyan 1.2, inda kuma a duk shekara ake cike giɓin da ake da shi na wanda ake shigo da shi kimanin na ƙalla dala biliyan 2.5.

Wani ƙiyasi da kamfanin ‘Reportlinker’ ya gudanar ya ce, buƙatar tumatir a shekara , za ta ƙaru zuwa tan miliyan 3.01 a 2028.

Jerin Manyan ƙalubalen da Ke Shafar Farashin Tumatir A Nijeriya:

1- Noman Tumatir daga Kaka Zuwa Kaka:

Hakan na haifar da tsadar farashinsa da kuma ƙarancinsa, musamman duba da cewa; nomansa a Arewacin Nijeriya, na faraway ne daga watan Nuwamba zuwa watan Maris, inda hakan ya sa ba a yin noman na gajeren zango, wanda kuma farashinsa ke raguwa a daidai lokacin.

Amma a lokacin damina, farashinsa na ƙaruwa ne sakamakon yadda yake yin ƙaranci.

 

2- Cututtukan da Ke Lalata Tumatirin da Aka Shuka:

ɓarkewar cututtuka, kamar irin su Tuta da ke lalata tumatirin da aka shuka, na shafar tashin farashinsa da kuma ƙarancinsa a Nijeriya.

 

3- Rashin Kayan Adana Tumatirin da Aka Noma:

Wannan na haifar wa da manomansa yin asara bayan sun  girbe shi, inda aka ƙiyasta kashi 40 cikin 100 na Tumatirin da aka girbe, ba ya kai wa ga masu sayensa kai tsaye, musamman ganin cewa; tuni ya riga ya lalace.

 

4- Rashin Samun Bayanai daga Kasuwanni:

Wannan ƙalubale na haifar wa da manomansa asara mai yawan gaske, saboda rasahin samun bayanai daga kasuwanni kafin su kai ga shi kasuwa, domin sayarwa.

 

5- ƙarancin Kayan Nomans  Tumatir Na Zamani:

Hakan na sanya manoman tumatiri gazawar samun amfani mai yawa tare da yin asara bayan sun girbe shi.

 

6- Faɗuwar darajar Naira da ƙarancin ƴan ƙwadagon da Ake dauka Haya:

Akasarin ƴan ƙwadagon da ake dauka haya daga ƙasashen da ke maƙwabtaka da Nijeriya, don yin aiki a gonakin da aka shuka tumatir a Kudacin ƙasar, saboda faɗuwar darajar Naira, suna komawa ƙasashensu ne.

 

7-  Rashin Samar da Tsare-Tsare Masu ɗorewa Ga Fannin:

Babban bankin ƙasa (CBN) a 2013, ya gudanar da taruka iri daban-daban tare da samar da tsare-tsare masu ɗimbin yawa ga wannan fanni, bisa hadaka da Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara da Ma’aikatar Masana’antu da Zuba Hannun Jari, domin daidaita fannin na noman tumatir a faɗin wannan ƙasa, amma duk da haka, haƙan bai kai ga cimma ruwa ba.

Kazalika, a 2022 zuwa 2026, gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro da tsari na ƙasa a kan noman wannan tumatir, musamman domin a rage asarar da manoma ke tabkawa, bayan girbi da kuma rage yawan shigo da shi daga ƙasashen ƙetare.

Sai dai, rashin wanzar da tsarin, ya sa lamarin ya koma tamkar ƴar gidan jiya.

 

8- Tsadar Kayan Noman Tumatir:

Kayan noman tumatir, musamman takin zamani da Iri, na da matuƙar tsada a Nijeriya, wanda idan manomansa suka shuka shi tare kuma girbe shi, ba sa iya samun wata ribar a zo a gani, inda hakan ke sanya farashinsa ya riƙa ƙaruwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abubuwa Biyar Game Da Kiwon Talotalo
Noma Da Kiwo

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

December 20, 2025
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa
Noma Da Kiwo

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

December 19, 2025
Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman
Noma Da Kiwo

Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman

December 14, 2025
Next Post
Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta

Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.