A cikin yanayin mastalolin tattalin arzikin da Nijeriya ke fuskanta, manyan kamfanonin gida Nijeriya sun dukushe tare da dakatar da ayyukansu a cikin wata 10 na shekarar 2023.
Matsaloli da dama suka taimaka wajen durkushewar kamfanonin sun kuma hada da karancin kudaden kasashen waje, karancin wutar lantarki, cunkoso a tashoshin jiragen Ruwan Nijeriya da kuma yawan haraji daga bangarori da dama sauran matsalolin sun hada da kuma uwa uba mastalar tsaro da ta addabi sassan Nijeriya.
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
- Kasar Sin Ta Harba Kumbon Dakon Kaya Domin Aikewa Da Kayayyaki Ga Tashar Sararin Samaniya
A daidai lokacin da kamfanonin cikin gida ke kurkushewa, wasu manyan kamfanonin kasashen waje sun bayyana aniyarsu na ficewa daga Nijeriya, kasar da ke yi wa kirari da babbar kasuwa a Afirka, manyan kamfanonin da suka bayyana aniyarsa na fita daga Nijeriya sun hada da ‘GladoSmithKline’ ‘Consumer Nigeria’, ‘Ekuinor’, Sanofi, Bolt Food, da kuma kamfanin ‘Procter & Gamble’.
Matsaloliin fa ake fuskanta basu bar kamfanonin cikin gida ba, wannan yake bayyana tsananin bukatar gwamnati ta kai musu tallafi don su farfado.
A sanarwa da BusinessDay ta fitar ranar Alhamis na makon jiya, ta zayyana kamfanoni 6 da suka daina aiki a cikin wata 10 na shekarar 2023, sun kuma kasance kamar haka:
- Kamfanin ‘Mayor Biscuits Limited (MABISCO)’ ya daina aiki ne a watan Maris 2023, an kuma kafa kamfanin ne a shekarar 2016, kamfanin na sarrafa tan 3.2 a awa daya yana kuma da masu rarraba musu kaya 300 a fadin Nijeriya.
- Kamfanin 54Gene: ya fara aiki ne a shekara 4 da suka wuce da jarin fiye da na dala miliyan 45, ya kuma durkushen ne a watan Satumba 2023.
- Kamfanin Lazarpay: an kafa kamfanin ne shekara 2 da suka wuce ya kuma durkushe a 2023 saboda lalacewar jari.
- Kamfanin kera allura na ‘Jubilee Syringe Manufacturing Company: a shekarar 2017 aka kafa kamfanin ya kuma durkushe a watan Disamban 2023 saboda wasu matsaloli da suka fuskanta na gudanarwa.
- Kamfanin DropD: ya fara aiki ne a watan Nuwamba na shekarar 2021 ya kuma durkushe a watan Disamba saboda dalilan da suka hada da mastalolin tattalin arzikin da Nijeriya ke fuskanta.
- kamfanin Okadabooks: kamfanin da ya jagoranci harkar saye da buga littafai ta na’u’rorin zamani ya durkushe ne bayan ya yi shekara fiye da 10 yana harkokinsa, cikin dalilansa na dakarar da aiki sun hada da matsalolin tattalin arziki da ya addabi Nijeriya dama duniya gaba daya.
A yayin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar mastalolin tattalin arzik, durkushewar wadannna kamfanoni ya tayar da tunannin halin da sauran kananan masana’antu suke ciki a Nijeriya, musamman kuma ya fito da bukatar samar musu da tallafi na musamman don ganin ba su durkushe ba.