A cikin Suratu Lahzabi, Aya ta 45 da 46, Allah (SWT) ya ce “Ya kai wannan Annabi, mu ne muka aiko ka ka zamo mai shaida a kan aikin al’ummarka, ka zama mai musu bishara da Aljanna, ka zama mai musu gargadi da wuta. Ka yi kira zuwa ga Allah da izininsa, kuma kai fitila ne mai haskakawa”.
Saboda Manzon Allah (SAW) ya samu wannan izini na musamman daga Allah, sai ya zama kiransa ga al’umma su karbi addini ya yi sauki fiye da na sauran Manzanni. Dukkan Annabawa masu kira ne da izinin Allah, amma dai babu wanda a cikin Alkur’ani aka fada ma sa karara cewa “shi mai kira ne da izini”, kamar Annabi Muhammad (SAW).
- Rahama, Jin Kai Da Hasken Manzon Allah (SAW)
- Duk Dangi Suna Alfahari Da Samun Manzon Allah (SAW) A Cikinsu
Annabi Nuhu (AS) shekara dubu ba hamsin ya kwashe yana kira zuwa ga Allah (SWT), amma mutum tamanin ya samu kadai suka yi Imani. Da ya sauka a Iraki da jirgin ruwansa, akwai garin da ya sauka ana ce ma sa “Baldatus samaniyna”, ma’ana “Garin mutum tamanin”, wato adadin wadanda ya tsallaka tare da su; sai kuma sauran dabbobi kawai.
Shi kuwa Sayyidina Rasulullah (SAW) da yake kiransa mai izini ne na musamman, shekara ashirin da uku kacal ya kwashe ya hada duk wannan alherin na Musulunci. A shekara goma sha uku da aka yi a Makka, kokari ake yi a fadi “La’ila ha illallah”, amma kafin a yi Hijira zuwa Madina Sallah ta sauka da ‘yan watanni. A shekara ta takwas bayan Hijira, Manzon Allah (SAW) ya dawo da sojoji dubu goma sha biyu ya bude Makka. Amma a shekara ta goma bayan Hijira da ya zo Hajji, ya zo da mutane dubu dari da ashirin da hudu (adadin yawan Annabawa). Duk wannan a cikin shekara 10 ne kacal bayan Hajira saboda sirrin wannan izinin na musamman. Shi kuwa Annabi Nuhu a cikin shekara dubu ba hamsin (950) ne ya samu mutum tamanin.
Don haka duk wani abu da aka samu izini na musamman a kai ya fi alheri da sauki. Yana daga alamar izini Allah ya saukake abin da aka yi nufin aiwatarwa ya zama ya gudana cikin sauki. Shi ya sa zikirai na darikun waliyyai ke tafiya a kan izini.
A karshen ma’anar ayar da muka kawo, Allah (SWT) ya ambaci Manzon Allah (SAW) a matsayin fitila mai haskakawa.
Haka nan, yana daga fadin Allah (SWT) a cikin Sura ta 94 da ya yi wa Annabi (SAW) kirari, “Ba mu ne muka yalwata kirjinka ba?”. Akwai magana maigirma a nan wurin, malamai sun ce a batun kera Annabi Adamu (AS) baki dayansa, Allah ya ce “hannunsa biyu (yadda ya dace da shi SWT) suka yi”, wato (Jamala da Jalalarsa a wurin Sufaye). Ayar tana cikin Suratu Dawud, Sura ta 38, Aya ta 75. Amma a cikin Alam nash’rah, Allah (SWT) ya ce shi ne ya goge kirjin Manzon Allah.
Malamai suka ce abin mamaki, wurin kera Annabi Adamu sukutum da guda dinsa; Allah ya ce hannayensa biyu suka yi, amma wurin goge kirjin Manzon Allah da buda shi, ba hannaye ne ba kadai suka yi, Allah ya nuna duk gaba dayansa (yadda ya dace da shi) ne ya yi; (SWT).
Suka ce, dalili shi ne, wannan halitta ta jiki babban abu be, sai dai Allah ya baiwa halittarsa dama a kai. Kamar misali, Allah ya baiwa likitoci ilimi da basira su yanke gabobin mutum su jona, su yi tiyata da sauran abubuwan da suke yi a jikin Dan Adam. A nan, Allah ya ba su dama a kan tasaruffi da jiki irin na Annabi Adamu. To amma bangaren abin da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a kirjinsa na sanya dabi’a mai kyau da halin Annabta (ba wai abu ne mai wuya a wurin Allah ba), wanene aka taba jin likitoci sun yi ma sa?
Kamar misali a ce ga wani yaro mara kirki mai halin banza babanshi ya kai shi wurin likitoci su yi ma sa tiyata su cire wannan halin na banza su sanya ma sa halin kirki da kyawawan dabi’u. Akwai likitan da yake yin wannan aikin?
Don haka maganar goge kirjin ta fi girma da matsayi fiye da na jiki. Na jiki ana yi, amma cire halin banza da munanan dabi’u a sanya halin kirki da dabi’u nagari sai dai Shi (SAW) da magadansa. Shi ya sa sau da yawa idan ka ji an ce “a kai yaro wurin malam wane”, to abu ya baci ne. Da yaron bai lalace ba cewa za a yi a kai shi makaranta.
Abin da ake nufi da “kirjin da aka yalwata na Manzon Allah (SAW)” a cikin ayar, tana nufin Zuciyarsa (SAW). Ma’ana kamar Allah (SWT) yana nufin cewa shi ne ya zuba kyawawan dabi’un nan na Manzon Allah (SAW) irin su hakuri, juriya, yafiya, tausayi, jinkai da sauran su.
Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA) ya ce “Allah ya yalwata kirjin Manzon Allah (SAW) da hasken Musulunci.”
Sahalu (RA) ya ce eh maganar Abdullahi haka ne, “Amma dai Allah ya haskaka kirjin Manzon Allah (SAW) da hasken Manzanci.”
Hasanul Basari (RA) ya ce ayar tana nufin “Allah ya cika kirjin Manzon Allah (SAW) – ma’ana zuciyarsa – da hukunce-hukunce da ilmi”. Alkur’ani baki dayansa yana cikin zuciyar Manzon Allah, kuma duk inda Alkur’ani yake akwai haske a wurin.
Allah (SWT) ya ce da zai saukar da wannan Alkur’anin a kan wani dutse, dutsen zai kekkece ya ragargaje komai girmansa. Amma sai ga shi Allah ya saukar da Alkur’anin a zuciyar Manzon Allah, zuciyar ta iya karbansa har ma ta sanyaya shi ta yadda zuciyoyin sauran mahaddata ma za su iya daukawa. Har zuwa yau Alkur’ani yana da zafi, amma taransifoman Manzon Allah ne ya sanyaya shi har mitoci (zuciyoyin mahaddata) suka iya karba.
Watakila kuma, an ce ma’anar ayar ta “Alam nashrah…” kuma ita ce “Allah ya tsarkake zuciyarka har ta zamo ba ta karban wasiwasi”, ma’ana shaidan ba shi da rabo a zuciyar Manzon Allah (SAW).
Fassarar Aya ta biyu ta cikin surar tana cewa “mun sauke maka wannan abin da ya nauyaya bayanka” kuma kila tana nufin “Allah ya dauke maka abin da ya shude na daga zunubinka”. Amma fa ba irin zunubin da aka sani na gama-gari ba ne. Shi wannan ana ce ma sa “tarku aula”. Misali, wasu mutane sun zo wurinsa (SAW) suka nemi izini ya yi musu afuwar zuwa yaki, ya san uzurin da suka bayar na karya ne amma saboda tausayinsa da kuma kasancewarsa ba mai dora wa mutane wahala ba; sai ya yi musu izini. A kan wannan, Allah (SWT) a cikin Alkur’ani ya ce “Allah ya yi maka gafara, don me ka yi musu izini?”. To kila irin wannan zunubin ne ake nufi.
Wata ma’anar ayar kuma tana cewa “Allah ne ya dauke maka nauyaye-nauyayen zamanin jahiliyya”, wato Allah ya sanya ma sa kin zamanin jahiliyya a zuciyarsa, wato kin gumaka da sauran nau’o’in daudar jahiliyya. Tarihi ya nuna cewa tun Manzon Allah (SAW) yana yaro idan mutum ya rantse da gunki sai ya tashi ya ba shi wuri.
A wata fassarar kuma, an ce ayar tana nufin “Allah ya saukake masa nauyin aike na manzanci”. Manzanci yana da nauyi sosai, shi ya sa da yawa idan Wahayi ya zo ma Annabi (SAW) sa’ilin da yake rike da hannun wani ko dafe da shi, sai a ji wanda aka rike din yana ihu. Wata rana Wahayi ya taba sauko wa Manzon Allah (SAW) a lokacin cinyarsa tana kan cinyar Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu), sai aka ji Sayyidina Aliyu yana ihu cinyarsa kamar za ta karye saboda nauyi, da shi da Sayyidina Abbas (RA) sun kasa daga cinyar Manzon Allah (SAW) saboda nauyin wahayi.
An ce idan yana kan rakumi Wahayi ya sauko ma sa, cikin rakumin yakan taba kasa saboda nauyin Wahayin. Amma duk da haka, shi Manzon Allah (SAW), Allah ya dauke ma sa wannan nauyin har ya isar da sakon da aka aiko shi da shi lafiya kalau.
Fassarar nan da muka yi bayaninta a kan nauyin Manzanci ayar take nufi, Malam Mawardi da Malam Sulamiyyu suka yi.
A wata fassarar Kuma, ayar ta “wa wada’ana anka wizhrak, allazhi ankadha zahrak”, tana nufin “mun kiyaye ka wanda ba domin haka ba da zunubi ya nauyaya bayanka”. Malam Samarkandi ya fadi wannan.
Ayar “wa rafa’ana laka zhikrak” Malam Yahya bin Adama ya ce ma’anarta Allah yana nufin “mun daukaka ambatonka da manzanci”. Wato idan an fadi Allah da kadaitakarsa sai a fadi Manzon Allah da Annabtarsa. Idan aka fadi “La’ilaha illallahu” sai a ce “Muhammadur Rasulullah (SAW)”. Babu yanda za a yi kuma a raba.
A wata ma’anar kuma ayar tana nufin, Allah ya ce “idan aka ambace ni sai a ambace ka tare da ni” kamar yadda aka buga misali da kalmar shahada a sama.
Kila kuma ana nufin a cikin kiran sallah idan aka ambaci Allah; “Ash’hadu an la ila ha illallah” sai a ambaci Manzon Allah “Ash’hadu anna Muhammadur Rasulullah (SAW)”. Haka nan a cikin Ikama.
Malam Alkadiy Iyad ya ce wannan tabbatarwa ne daga Allah wanda sunansa ya daukaka cewa, ya yi wa Manzon Allah ni’ima mai girma da daukaka a wajensa. Allah ya ce ya yalwata zuciyar Manzon Allah (SAW) da Imani da Shiriya, ya kuma yalwace ta don haddace ilmi da daukar hikima (ma’arifa).
Kuma dama Allah ya ce “za mu karanta ma ba za ka manta ba”. A lokaci daya Allah (SWT) ya saukar da Surar Bakara kuma Manzon Allah (SAW) ya haddace ta ya karanta wa marubuta suka rubuta.