Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.
Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1446 a bara, lissafin zai ba ka cewa a baran Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1499 da haihuwa. A bana kuma zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa kenan.
- Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (6)
- Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu idan Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal mai zuwa lokacin da Manzon Allah zai cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron kasa yanzu ya kara wasu shekaru 500 a raye.
A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).
Farkon Mutanen Madina Da Suka Musulunta Kafin Hijira Da Yadda Suka Yada Musulunci
Allah Ta’ala shi ya shisshirya abubuwansa. Ya aiko Manzon Allah (SAW) yana da shekara 40. Tun abu yana cikin gida har ya fito waje, ya game gari a boye-a-boye saboda manyan shegun gari irinsu Abu Jahli da Walidu bin Mugira. An yi shekara shida Sayyidina Hamza ya Musulunta, Sayyidina Umar ya musulunta aka cika mutum 40 wadanda suka musulunta.Tun da mutum biyun nan suka musulunta dama su ake jin tsoro sai Musulunci ya kara samun karfi. Sayyidina Umar ya ce a fito, mutanen gari suna ganin haka suka ce ‘eh, lallai, Muhammadu ya raba mana gari, ya kwashi rabi ya bar mana rabi’ saboda musuluntar wadannan manyan sahabban biyu. Tun daga rannan mutane suka rinka shiga Musulunci har zuwa lokacin da Manzon Allah (SAW) ya tura Sahabbansa su 70 Hijira zuwa Habasha. Zuwa shekara ta kusan 11 da aiko Manzon Allah (SAW) wadanda suka musulunta ba su fi dari da wani abu ba, amma Manzon Allah bai damu ba, don ya san Musulunci sai ya game duniya bakidaya. Idan an samu mutum daya ya zama na Allah ya fi taron yuyuyu.
Su kafiran sun ce mutumin nan (Manzon Allah SAW) yana da hankali, domin ya tura mutanensa da suka musulunta ana muzguna musu zuwa Habasha. Kuma Habasha matattara ce ta kasuwanci. Suka tura wasu wakilansu su je su dawo da su (sahabban), sai kuma Sarkin Habasha Najjashi ya zama nasu, ya ce duk wanda ya taba su ni ya taba. Kafiran suka ce ai shikenan, dama tsafi (Manzon Allah) yake yi, don ga shi har ya gama da Sarki Najjashi. To, har zuwa lokacin dai Manzon Allah yana Makka, don Nana Kahadijah da Abu Dalib masu taimakon Manzon Allah suna nan. Bayan rasuwarsu, sai Allah ya zo wa Manzon Allah da mutanen Madina.
Kodayake bayan Makka ta yi kunci, Manzon Allah ya tafi Da’ifa, can ma dai abin ba dadi, to sai ya zama kamar Allah yana wa Manzon Allah ishara da barin wurin saboda rashin dadin zaman yankin na Makka. Mutane masu girma su shida daga Madina (Banu Khazraju) suka zo masa (SAW). Akwai As’adu bin Zurarata, Aufu binil Harisi bini Rufa’ata, Rafi’u bin Maliki bin Ajalani, Utbatu bin Amiri bin Udaidata, Ukbatu bin Amiri bini Nadi, da Jabiru bin Abdullahi bini Riyadi (Masoyin Manzon Allah SAW). Sun zo aikin Hajji. Su dama mutanen Madina akwai Yahudawa da suka cika musu gari suna jiran Annabin karshen zamani ya zo, saboda sun karanta cewa za a haifeshi a Makka, amma zai zauna a Madina. Sai suka zabi su je Madina domin nan ne mazauninsa, maimakon Makka inda aka haife shi. To kuma da Annabi (SAW) ya zo duk sai suka yi ma abin fenti, suka ki karbar gaskiya. Da yawa wannan yakan samu masu cewa suna jiran abu ya zo, abin zai zo sai su yi masa fenti su yi inkari su karyata. Yahudawan suka ce Annabin karshen zamanin ba Balarabe ba ne, a cikinsu ne Yahudawa zai zo. Kuma idan ya zo za su kashe Larabawa irin yadda aka kashe Adawa (kamar ba da rahama zai zo ba).
To da Sahabban nan Ansaru shida suka zo Makka Annabi (SAW) ya isar musu da sakon kansa sai suka gane shi, suka yi shawara suka ce tabbas shi ne Annabin nan na karshen zamani, suka yi imani da shi. Da Manzon Allah ya nemi ya je Madina a lokacin suka bukaci ya dan dakata, saboda sun ce ba su dade da yin yakin Bu’asu ba (yakin basasa). Da yake Allah ya tsara zuwan Manzon Allah Madina sai aka kakkashe manyan da suke hana shiga garin a cikin yakin. Sahabban suka ce za su koma su isar da sakonsa (SAW) kafin daga bisani a ga yadda za a yi.
Bayan shekara guda da yin wannan, wato a shekara ta 12 da aike (manzanci), sai kuma wasu mutum bakwai suka karu daga Madina. Sai suka zama su 12 suka zo, mutum biyar wadanda na bara (tun da Jabir bai zo ba lokacin) da kuma karin mutum bakwai suka musulunta a hannun Manzon Allah (SAW). Su ne Mu’azu binil Harisi bin Afra’a, Zakawani bin Abdukaisin Azzuraifiyyu, Ubadatu bin Samiti (ya haddace Kur’ani a gaban Manzon Allah), Yazidu bin Sa’alabatal Balawi, Abbasu bin Ubadata bin Nablata. Su biyar din dukkansu daga Kabilar Khazraju ne. Yanzu in an hada da wadanda suka zo bara, ‘Yan Kabilar Khazraju sun zama su 11. Sai mutum biyu cikon wadanda suka zo a shekara ta 12 su bakwai su ne: Abul Haitamu ibnit Tayyahani daga Banu Abdul’ash’hari sai Uwaibu bin Sa’idata, su kuma daga Kabilar Ausu. Suka yi mubaya’a ga Manzon Allah (SAW) cikin dare a Minna a kan ba za su tara Allah da komai ba (fatahi ya samu kenan), ba za su yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe ‘ya’yansu ba, ba za su yi kagen karya ba (ko a gabansu ko a karkashinsu), ba za su sabi Manzon Allah ba, sun ji-sun-gani wurin bin Manzon Allah a lokacin yalwa da lokacin tsanani, da dora Manzon Allah a kansu, da rashin jayayya ga duk wanda Manzon Allah ya damka masa wani abu a kansu, kuma za su fadi gaskiya a duk inda suke ba tare da tsoron zargin mai zargi ba (sai dai rarrashi amma ba ha’inci ba). Manzon Allah ya ce musu, idan kun cika wadannan abubuwan kuka mutu a kai, to Aljanna taku ce. Wanda kuma ya dan saba wani abu a ciki (daga cikinku) lamarinsa yana wurin Allah. Idan Allah ya so ya azabtar da shi, idan ya so ya masa rangwame, ba zancen yaki a wannan.
Shikenan Manzon Allah ya sallame su za su koma Madina, ya basu izinin yin kiran mutane zuwa ga Allah. Manzon Allah ya nada musu As’adu bin Zurarata a matsayin Liman. Da za su tafi sai suka nema daga Manzon Allah ya ba su wanda zai rika koya musu Alkur’ani, sai ya ba su Mus’abu bin Umairul Abdari. Halitta mai yawa ta musulunta a hannun Mus’abu bin Umair, ciki har da Sa’adu bin Mu’azu wanda ya zama kamar Sayyidina Abubakar a cikinsu saboda himmarsa, da kuma Usaidu bin Khudairun. Saboda musuluntar wadannan mutanen (biyu), duk kabilar Banu Ash’hari (daga Ausu) rana daya suka musulunta mazansu da matansu gabadaya in banda mutum daya da ake ce masa Usairimu, sunansa Amru bin Sabiti bin Wakshi. Shi kuma sai a ranar yakin Ukhudu, a rannan ya musulunta, rannan ya tafi yaki kuma a rannan ya yi shahada. Ita wannan kabila Allah ya yi mata wani irin alkhairi ba a samu munafiki ko daya a cikinta ba.
Sahabban nan na Manzon Allah (‘Yan Madina) suka yi ta kira zuwa ga Allah, kafin shekara guda, an samu musulmi fiye da mutum 70 a Madina (Alhamdu lillah). An samu mutum shida a shekara ta farko (da ‘Yan Madina suka zo wurin Annabi SAW suka yi imani), a shekara ta biyu an samu mutum 12, yanzu kuma a shekara ta uku an samu fiye da 70. A shekara ta 13 kuma (shekarar Hijira) da aka yi Mubaya’ar Akaba, Kabilun Ausu da Khazraju sun zo su 73 maza, da mata biyu, su 75 kenan suka yi mubaya’a ga Manzon Allah (SAW). A wannan lokacin labarin musulunci ya shiga kusan ko wane gida na Larabawa a Madina. To, daga nan ne Sahabban na Madina suka ce wa Manzon Allah yanzu ya iya zuwa Madina, suka yi mubaya’a gare shi cewa za su kare shi, za su kare lamarin Allah.
Har Annabi (SAW) ya yi Hijira musulmin duniya ba su cika 200 ba in an hada jimilla da Sahabban da suka yi Hijira zuwa Habasha, da na Makka da na Madina. An shekara 13 ana kira zuwa musulunci amma wadanda aka samu kenan, amma a lokacin Hajjin bankwana, Manzon Allah ya je Makka da mutum 124,000. A yau kuma musulunci ya game duniya, akwai Musulmi sama da biliyan daya, Alhamdu lillah!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp