Mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya ce, ya yafe wa ‘yan jam’iyyar NNPP kan zargin da suka yi wa kwamitin kungiyoyin Arewa na son fifita, Atiku Abubakar kan Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Dakta Hakeem ya mayar da wannan martanin ne kan wani taro da kungiyoyin Arewa su kayi a Arewa House dake Kaduna a kwanakin da suka gabata inda suka gayyaci dukkan ‘yan takarar shugaban kasa amma na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso bai samu halartar taron ba.
Daga bisani, sai ‘yan Jam’iyyar su kayi zargin cewa, an shirya taron ne don fifita dan takara a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar kan dan takara a Jam’iyyar NNPP, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Taron dai, an shirya shi ne, don jin ta bakin kowanne dan takara, kan tagwarmashin da zai baiwa yankin in ya samu nasarar lashe zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp