‘Yan adawa sun mayar da martini kan zanga-zangar da aka gudanarwa a fadin kasar nan, sannan sun kuma mayar da mar-tini kan jawabin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi kan zanga-zangar.
Wasu jiga-jigan ‘yan adawa da suka hada da Dakta Umar Ardo, Hajiya Naja’atu Mohammed, Dakta Salihu Lukman da kuma Farfesa Usman Yusuf, sun goyi bayan wadanda suka shirya zanga-zangar a fadin kasar nan; kan halin kunci a Nijeriya.
- Za Mu Raba Wa Talakawa Kyautar Kudi – Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da su-ka sanya wa hannu, inda suka bayyana fatansu na ganin cewa; zanga-zangar za ta haifar da sauye-sauyen siyasa da tsari a Arewa da kuma Nijeriya baki-daya.
Kazalika, sun tabbatar da cewa; ‘yancin da tsarin mulki ya ba wa dukkan ‘yan kasa damar gudanar da zanga-zanga, sannan kuma sun yarda cewa; dalilin zanga-zangar adawa da tsarin na da inganci kuma ya dace, don haka suka tsaya tsayin daka wajen ganin sun yi amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zangar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shuga-ban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya yi Allah wadai da amfani da harsashi kan ‘yan kasa da ke zanga-zangar lumana, kan matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin ar-ziki.
Atiku ya yi wannan kakkausan lafazi ne, yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a Nijeriya, inda wasu jihohi aka samu hargitsi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar kamar Kano da Abuja da kuma Kaduna.
Zanga-zangar da aka fara gudanarwa daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta, an samu rahotannin asarar rayuka, lalatawa tare da wawure dukiyar gwamnati da al’ummar kasa a wasu jihohin kasar nan.
Atiku ya bayyana matakin jami’an tsaro na yin amfani da harsashi kan masu zanga-zangar da cewa, “abu ne mai muni da ya yi kama da zamanin mulkin kama-karya na soji.”
Haka nan ita ma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce, Shugaba Bola Tinubu; sam bai damu da halin da ‘yan kasar ke ciki ba, duk da zanga-zangar da ake gudanarwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, wadda ta samu sa hannun sakataren yada labarunta na kasa, Debo Ologunagba, PDP ta ce; jawabin Tinubu ya nuna yadda karara APC da Shugaba Tinubu ba su damu da halin kuncin da al’ummar kasar ke ciki ba.
Zanga-zangar, wadda ta fara a ranar Alhamis ta rikide zuwa ri-kici a wasu jihohin, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da duki-yar al’umma.
Tinubu dai ya bukaci masu zanga-zangar da su janye tare da bude kofar yin zama, domin tattaunawa.
Yanzu haka dai, al’amura na kara ta’azzara a wasu jihohi kamar Filato, Kaduna da kuma Bauchi, inda jihohin suka sanya dokar hana fita a ranar Litinin.
A Jihohin Kano, Yobe da Katsina kuwa; gwamnatocin jihohin sun sassauta dokar hana fitar ne duk da cewa, ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar.
PDP ta ce, abin da Tinubu da jami’yyarsa ke nuna wa ‘yan Nijer-iya; alama ce ta cewa kasar ba a gabansu take ba.
Haka kuma, ‘yan adawan sun caccaki Shugaban Kasa Tinubu; kan jawabin da ya gabatar wa ‘yan kasa kai tsaye a safiyar La-hadi.
Jam’iyyar PRP a nata bangaren kuma, ta bukaci Shugaban Kasa Tinubu ya saurari bukatun masu zanga-zangar ta hanyar rage kudin gudanar da gwamnatinsa tare da kawar da cin hanci da rashawa da kuma almubazzaranci.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Dakta Falalu Bello; shi ya bay-yana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya cewa; hakki ne da ‘yan kasa suke da shi na yin zanga-zanga da kuma gudanar da ‘yancinsu.
Sai dai, ya bukaci masu zanga-zangar su gudanar da ita cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.
Haka zalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi; ya koka da gazawar gwamnatin tarayya wajen magance bukatun da suka rura wutar zanga-zangar yunwa a fadin kasar baki-daya.
Obi ya bayyana hakan ne, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita a ranar Litinin, inda ya bukaci shugaban kasar ya ni-santa kansa daga wasu mutanen da suka kewaye shi marasa gaskiya da kishin kasa.
Obi ya kuma bukaci gwamnati, da ta yi kokarin gano masu ai-kata laifukan da ke yunkurin kawo cikas ga zanga-zangar ta hanyar satar dukiyar jama’a da sauran munanan dabi’u da ku-ma kare wadanda ke aiwatar da hakkinsu na dimokuradiyya.
Shi ma Atiku, ya caccaki jawabin shugaban kasar, inda ya ce; jawabin na cike ne da rudani, sannan ya kasa warware matsalolin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Atiku, wanda ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ya ce, jawabin shugaban kasar babu abin da ya yi illa kara tunzara masu zanga-zangar.