Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ta daura damarar dawo wa da kima da martabar fina-finan Hausa a idon duniya ta hanyar daidaita yadda ake shirya su domin su dace da al’adar Malam Bahaushe da zamantakewar magidanta a kasar Hausa.
- Hajji 2024: Sarki Salman Na Saudiyya Ya Bai Wa Mahajjata Kyautar Al-Æ™ur’ani Mai Girma
- Kwamitin Tsakiyar Jami’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Ya Kira Taron Ba Mambobinsa Ba
A kan wannan ne jami’ar ta shirya taron masana da kwararru kan tasiri, matsaloli da alkiblar da ya kamata fina-finan su dosa, wanda aka gudanar ta manhajar zoom a kafar sadarwar intanet.
- Rikicin Sarautar Kano: Yadda Gwamnatin Abba Ta Sauya Alkibla
- A Watan Mayu Za A Bude Bikin Baje Kolin Motoci Na Afrika A Legas
- Amurka: Sarkin Leken Asiri Na Neman Habaka Karfinta
Masana da masu ruwa da tsaki a farfajiyar ilimi sun tattauna tare da fitar da tsaki da tsakuwa a taron da aka yi wa taken “Fina-fiinan Hausa da Zamantakewar Magidanta: Ina Aka Dosa?” a karkashin jagorancin Farfesa Abdallah Uba Adamu na tsangayar sadarwa da ke jami’ar Bayero, Kano.
Shehunan Malaman jami’a, fitattun malaman addini da masu ruwa da tsaki a sha’anin fina-finan Hausa da suka tattauna a taron na yini daya su ne, Aliyu Muhammad Bunza wanda shi ne Farfesan al’adun Hausawa na farko a duniya, wanda ya gabatar da mukala mai taken “Zamantakewar Auren Hausawa da Al’adun Hausawa.” Haka ma Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi ya gabatar da takarda mai taken “Samuwar Fina-finai da Canjin Manufarsu da Aka Samu.”
Fitaccen maruubuci, jarumi kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ado Ahmed Gidan Dabino wanda shi ne shugaban kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Jihar Kano (MOPPAN) ya gabatar da mukala mai taken ‘Manufa da Gudunmuwar Fina-finan Hausa ga Zamantakewar Hausawa.”
Ita kuwa Hadiza Salihu Koko daga kwalejin ilimi ta Shehu Shagari ta gabatar da kasida mai taken “Tasirin Fina-finan Hausa ga Zamantakewar Ma’aurata,” sai Sheikh Aminu Daurawa, shugaban Hukumar Hisbah Kano ya gabatar da takardar da ya rada wa sunan “Zamantakewar Ma’aurata a Addinin Musulunci Akasin yadda take a Fina-finan Hausa.”
Masanan sun cimma matsayar cewar fina-finan Hausa da aka fara shiryawa a
can baya an tsara su da gina su da haska su a akwatunan talabijin a bisa ga manufar fadakar da al’umma da ilmantar da su a kan shirye- shiryen ayyukan gwamnati akasin manufofin neman kudi na fina-finan wannan zamani.
“An lura da cewa al’umma suna taka muhimıniyar rawa wajen yaduwa da yawaitar kallon wadannan fina-finan Hausa da amfani da darussan da suke cikinsu masu alfanu da akasin haka.”
Tatttaunawa a taron an samu nasarar gano gurbatacciyar hanyar da masu shirya fina-finan suke ake yi wadda ke bukatar gyara domin kuwa sun cimma matsayar cewar, “fina-finan Hausa na wannan zamani sun saba wa al’adun Hausawa na asali baki daya na zamantakewa da kunya da sutura da tarbiyya, kuma suna haddasa matsalolin rashin fahimta da rabuwar aure atsakanin ma’aurata.”
Duka baya ga wannan kusoshin taron sun yi iyo da ninkaya tare da fito da shawarwari da hanyoyin da suke ganin su ne mafita wajen shirya fina-finan da Hausa da Hausawa za su yi alfahari da su a duniyar Malam Bahaushe, wadanda suka hada da: “shirya fina-finan Hausa wadanda suke
nuna darussan kyawawan al’adun zamantakewar auren Hausawa na tarbiyya da kunya da biyayya tsakanin ma’aurata da ‘ya’yansu kamar yadda wasannin kwaikwayo na da suka nuna.”
A cewarsu, “Bai kamata fina-finan Hausa na wannan zamani su mayar da hankali ga sana’ar neman kudi kawai ba, akasin fadakarwa da ilmantarwa da koyar da kyawawan al’adu da dabi’un Hausawa. Akwai bukatar magidanta da sauran al’ummar Hausawa su kauce wa kallon fina-finan Hausa na wannan zamani wadanda suka saba wa al’adu da addini da tarbiyyar Hausawa, wannan zai rage yaduwar fina-finan da amfani da miyagun darussan da ke cikinsu.”
Jagororin taron wadanda suka bayyana cewar za a ci gaba da gudanar da taron a nan gaba sun kuma ba da shawarar cewar, masana da manazarta su mayar da hankali sosai wajen rubutawa da shirya fina-finan Hausa masu koyar da kyawawan al’adu da dabi’un Hausawa, Gwamnati kuwa ta tallafa wajen daukar nauyin samar da su da yada su.”