Waɗanda suka yi garkuwa da shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Ose ta jihar Ondo, Hon. Nelson Adepoyigi, sun sake yin garkuwa da mutane biyu da suka kai musu kuɗin fansar miliyan ₦5 da kayan abinci.
Bayan sun sace Adepoyigi a ranar Litinin da dare, masu garkuwar sun rage buƙatunsu daga miliyan ₦100 zuwa miliyan ₦5 tare da buƙatar kayan abinci domin sakin shugaban.
- NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m
Duk da haka, bayan mutanen biyu – Bayode Loco da Isimeri – suka kai kuɗin da abincin, masu garkuwar sai suka sake kama su kuma suka ƙara buƙatar miliyan ₦30 na fansa domin sakin dukkanin mutanen uku.
Wata majiyya da ba ta son a bayyana sunanta ta bayyana cewa lamarin ya sa iyalin da abokan siyasar wanda aka yi garkuwa da shi sake firgita.
Shugaban ƙaramar hukumar Ose, Hon. Kolapo Oja, ya tabbatar da cewa an tattauna kan rage kuɗin fansar zuwa miliyan ₦5 da buƙatar kayan abinci, amma ya nuna damuwarsa kan yadda lamarin ya koma.
Adepoyigi an sace shi ne da ƙarfe 10:00 na dare yayin da yake ƙoƙarin ajiye motarsa a gidansa da ke Ifon.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp