Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da cewa Hakimin kauyen Zira da ke Toro a Jihar Bauchi, Yahaya Saleh Abubakar da dansa, Habibu Yahaya sun kubuta daga hannun wadanda suka sace su.
Kazalika, shi ma tsohon sakataren hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, (NFF), Alhaji Sani Ahmed Toro, da tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila gami da Alhaji Isa Jah da aka yi garkuwa da su, su ma sun samu ‘yancinsu.
- Adamu Yaki Cewa Uffan Kan Mika Sunan Lawan Da Akpabio Ga INEC
- Hajjin Bana: Sarkin Musulmi Ya Nemi Mahajjata Su Yi Wa Kasa Addu’ar Shugabanni Na Gari A 2023
Kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ne ya tabbatar da batun kubutar nasu a ranar Talata, ya ce, dukkaninsu su na cikin koshin lafiya kuma cikakken bayani zai zo daga baya.
Idan za a iya tunawa dai Sarkin na kauyen Zira, Malam Yahaya da dansa sun shiga hannun masu garkuwa ne a ranar Asabar da daddare.
Har wa yau, wakilinmu ya labarto cewa, tsohon sakataren hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, Sani Toro da Yila hadi da Jah sun samu ‘yancinsu ne a ranar Talata wajajen karfe biyar na Asuba kamar yadda majiyoyi suka shaida.
Wani makusancin wadanda lamarin ya shafa, ya shaida cewar sun kubuta cikin koshin lafiya amma za a kaisu asibiti domin tabbatar da halin lafiyarsu.
An labarto cewa, Sani Toro da Yila tare da Jah an yi garkuwa da su ne lokacin da suke kan hanyarsu na dawowa daga Abuja zuwa Bauchi a daidai kan hanyar Akwanga zuwa jihar Nasarawa bayan sun halarci daurin auren dan tsohon Shugaban NFF, Aminun Maigari a Abuja ranar Asabar din da ta wuce.
Daga baya masu garkuwan sun bukaci kudin fansa har naira miliyan 150 kafin su sake wadanda suka kama. Sai dai babu wani cikakken bayanin nawa aka fiya kafin sake su zuwa yanzu.